Tambuwal ya rantsar da sabon mataimakinsa

Tambuwal ya rantsar da sabon mataimakinsa

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya rantsar da Alhaji Mannir Dan'iya, a matsayin sabon mataimakinsa biyo bayan murabus din Alhaji Ahmed a ranar 13 ga watan Nuwamba.

Da yake jawabi yayin rantsar da sabon mataimakin a yau, Juma'a, Tambuwal ya ce har yanzu akwai kyakykyawar alaka tsakaninsa da tsohon mataimakin nasa.

"Akwai fahimtar juna tsakani na da tsohon mataimakina.

"Ina kira ga matasan jihar Sokoto da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a ga jam'iyyar PDP a zaben 2019," a cewar Tambuwal.

Tambuwal ya rantsar da sabon mataimakinsa
Tambuwal
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Aliyu ya yi murabus ne domin samun damar mayar da hankali a kan yakin neman zaben takarar kujerar gwamnan jihar Sokoto da ya ke yi a jam'iyyar APC.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar 'yan sanda biyu da mambobin kungiyar Biyafra sun mutu yayin wata arangama a yau, Juma'a, a garin Nnewi dake jihar Anambra.

Sai dai hukumar 'yan sanda a jihar ta Anambra sun ce dan sanda daya ne ya mutu yayin da DPO din ofishin yankin ke kwance a asibiti bayan ya samu raunuka yayin artabun.

DUBA WANNAN: Tone-tone: Jonathan ya bayyana gwamnonin da su ka ci amanarsa a 2015

Da yake magana da majiyar mu ta wayar tarho, Mike Okoli, mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da aiyuka a jihar Anambra, ya ce, "zan iya baku tabbacin cewar mun yi rashin jami'in dan sanda guda mai mukamin sufeto. Sannan DPO din da su ke tare ya samu raunuka, kuma yanzu haka yana asibiti. Wannnan shine abinda na sani."

Rahotanni sun bayyana cewar 'yan kungiyar ta Biyafra sun kewaye garin Nnewi domin gudanar da zanga-zangar neman a gudanar da zaben raba gardama da zai ba su damar kafa kasar Biyafra ta 'yan kabilar Igbo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng