Danlami Gemu, shugaban yan bindigan da suka kai hari Katsina ya shiga hannu

Danlami Gemu, shugaban yan bindigan da suka kai hari Katsina ya shiga hannu

Shugaban gungun yan bindiga miyagu da suka kai hari a kauyen Gora dake jahar Katsina, Danlami Gemu inda suka kashe akalla mutane goma sha daya, ya shiga hannun jami’an rundunar Yansandan jahar Katsina, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito a yayin wannan hari da yan bindigan suka kai, sun kashe mutane goma sha daya, wanda a cikinsu Gemu shi kadai ya kashe mutane uku da basu ji ba, basu gani ba, a ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Dubun wani Malamin Islamiyya dake danne kananan dalibai a gidansu ta cika a Kano

Sai dai a yayin da yansanda suka yi kokarin dauke Gemu daga karamar hukumar Safana don mayar da shi zuwa babban ofishin Yansanda dake garin Katsina, an samu wasu daruruwan matasa da suka tare hanya, suna neman Yansanda su mika musu shi don su kashe shi.

Da kyar da sudin goshi aka shawo kan matasan, tare da gudunmuwar shugaban karamar hukumar Safana, Abba Safana, wanda yayi kira ga matasan da su kwantar da hankulansu, sa’annan ya gargadesu dasu guji daukan doka a hannunsu.

Haka zalika koda gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya kai ziyarar jaje ga al’ummar kauyen Gora, an jiyo shugaban karamar hukumar yana tabbatar ma jama’an kauyen cewa suyi hakuri, doka za tayi halinta akan Gemu.

A wani labarin kuma an sake samun barkewar rikici tsakanin wasu gungun miyagun mutane yan bindiga masu garkuwa da mutane, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutum guda daga cikinsu, kamar yadda shugaba Abba Safana ya bayyana.

“A jiya jiyan nan ma wasu yan bindiga guda biyu sun samu matsala tsakaninsu, wanda ya janyio cacar baki ta kaure a tsakaninsu, hakan yasa a cikin fushi guda daga ciki ya dirka ma abokinsa bindiga, nan take ya fadi matacce. Don haka mu dage da addua Allah ya cigaba da sanya fitina a tsakaninsu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel