Maraici: Fadar shugaban kasa ta farkewa Atiku laya a kan tashi babu iyaye, hotonsa da iyayensa

Maraici: Fadar shugaban kasa ta farkewa Atiku laya a kan tashi babu iyaye, hotonsa da iyayensa

A yayin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayar da dama ga 'yan siyasa domin fara yakin neman zabe, 'yan takara sun fara sakin manufofinsu da kalamai ma su dadi domin jan ra'ayin ma su kada kuri'a.

Sai dai a yayin da 'yan takara ke neman goyon bayan jama'a, su kan yi kalaman da ba gaskiya bane. 'Yan siyasar na yin irin wadannan kalamai ne domin jama'a su tausaya ma su, su goya ma su baya.

Wani batu da ya dade da zagayawa a Najeriya shine maganar maraicin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Atiku ya sha fadi cewar ya tashi babu mahaifi kuma ba tare da wasu 'yan uwa ba. Hakan ya saka shi tashi cikin mayuwacin halin rayuwa, da sai ya je ya yi ciyawa ko icen sayarwa domin daukan nauyin mahaifiyar sa da karatunsa.

Maraici: Fadar shugaban kasa ta farkewa Atiku laya a kan tashi babu iyaye, hotonsa da iyayensa
Maraici: Fadar shugaban kasa ta farkewa Atiku laya a kan tashi babu iyaye, hotonsa da iyayensa
Asali: Twitter

Amma abin tambayar a nan shine; da gaske ne cewar Atiku ya tashi ne a matsayin maraya?

DUBA WANNAN: Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa

"Na tashi ne a matsayin maraya, na sayar da itace a garin Jada, jihar Adamawa, domin na taimaki rayuwata, yau ga shi Allah ya daukaka ni," a cewar Atiku yayin wata ganawar kai tsaye da ya yi da ma su bin shafinsa na Facebook. Jaridu da dama sun wallafa wadannan kalamai na Atiku, cikinsu har da jaridar Legit.ng.

Shafin samar da bayanai na Wikipedia ya bayyana cewar an haifi Atiku a ranar 25 ga watan Nuwamba a shekarar 1946. Sunan mahifinsa Garba Abubakar, mahaifiyar sa kuma Aisha Kande. An haife shi ne a garin Jada, jihar Adamawa.

Atiku ya kasance da daya tilo wurin iyayensa bayan mutuwar 'yar uwarsa tun tana jaririya.

Maraici: Fadar shugaban kasa ta farkewa Atiku laya a kan tashi babu iyaye, hotonsa da iyayensa
Maraici: Fadar shugaban kasa ta farkewa Atiku laya a kan tashi babu iyaye, hotonsa da iyayensa
Asali: Twitter

Mahaifin Atiku ya rabu da mahaifiyar sa kafin rasuwar sa a shekarar 1957, sannan mahaifiyar sa ta sake yin wani auren kafin ta rasu a shekarar 1984 bayan ta kamu da ciwon zuciya. Wannnan labari na mutuwar mahifiyar sa na nan a cikin littafin da ya rubuta mai taken "MY LIFE".

Yanzu haka Shekarun Atiku na haihuwa 72, hakan na nufin cewar yana da shekaru 38 lokacin da mahaifiyar sa ta rasu.

DUBA WANNAN: Kisan sifeto: 'Yan sanda sun kama 'yan Biafra 34 a Nnewi

Wasu da yawa na ganin cewar batun cewar Atiku ya tashi maraya ba gaskiya ba ne, yana fadar hakan ne domin jama'a su tausaya ma sa.

Hakan ne ya saka fadar shugaban kasa bayyana cewar Atiku ya shirga karya ne don jawo hankalin 'yan Najeriya su saki jiki da shi tare da amincewa cewar shi ma talaka ne ko kuma ya san talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel