Gwamna Bello zai bayar da Ladan N100m ga bayanai kan makasan Hadimin sa

Gwamna Bello zai bayar da Ladan N100m ga bayanai kan makasan Hadimin sa

Mun samu cewa gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya sha alwashin tanadar da N100m ga duk wani mahaluki da ya bayar da bayanai da za su taka rawar gani gami da tasiri wajen cafke miyagun mutanen da ke da hannu cikin kisan gillar hadimin sa, Mallam Yusuf Adabenege.

Gwamna Bello kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito ya bayyana cewa, zai bayar da wannan makudan kudi na N100m ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su taimakawa hukumomin tsaro wajen cafke 'yan ta'addan da suka kawar babban mai ba shi shawara na musamman kan harkokin al'adu da yawon bude idanu.

Cikin wata sanarwa da sa hannun shugaban cibiyar watsa labarai da rahotanni na jihar, Alhaji Abdulmalik Abdulkarim, gwamna Bello ya yi wannan alwashi ne a garin Okene na jihar yayin ta'aziyya ga iyalan Hadiminsa da kaddara ta rigayi fata a kansa.

Sanarwar kamar yadda shugaban cibiyar ya bayyana ta shawarci duk wani mai makamancin wannan bayanai da gwamnatin jihar ta bukata ya yi gaggawar neman ganawa tare da gwamna Bello ta hanyar layinsa na wayar tarho ko kuma hukumar tsaro ta kurkusa.

Gwamna Bello zai bayar da Ladan N100m ga bayanai kan makasan Hadimin sa
Gwamna Bello zai bayar da Ladan N100m ga bayanai kan makasan Hadimin sa
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Mallam Adabenege ya riga mu gidan gaskiya da misalin karfe 6.45 na yammacin ranar 16 ga watan Nuwamba, inda 'yan ta'adda rike da bindigu suka katse ma sa hanzari tare da Direbansa a babbar hanyar Obehira ta garin Okene.

KARANTA KUMA: An yankewa wani Barawon Keke 'Dinki hukuncin dauri na watanni 14 a jihar Sakkwato

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, samun wannan rahoto ya jefa gwamna Bello cikin yanayi da hali na damuwa da ya sha alwashin gwamnatinsa ba za ta gaza ba wajen bankado ma su hannun cikin wannan muguwar aika-aika.

Kazalika jaridar ta kuma ruwaito cewa, rashin imani ya sanya wasu matsafa sun kwakule idanun wani karamin Yaro a kauyen Agaza da ke karamar hukumar Keana ta jihar Nasarawa a Arewacin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel