Rikicin kabilanci: Jerin unguwanni 5 da gwamnatin jahar Bauchi ta sanya ma dokar ta ɓaci

Rikicin kabilanci: Jerin unguwanni 5 da gwamnatin jahar Bauchi ta sanya ma dokar ta ɓaci

Gwamnatin jahar Bauchi ta sanar da sanya dokar ta baci da zata hana shige da fice a wasu sassan jahar guda biyar biyo bayan ballewar rikicin kabilanci daya sauya ya zama na addini a jahar tun a ranar Litinin 19 ga watan Nuwamba, inji rahoton Daily Trust.

Gwamnan jahar Muhammad Abubakar ne ya bayyana haka cikin jawabin da yayi ma al’ummar jahar a ranar Talata 20 ga watan Nuwamba, inda yace gwamnatin ta yanke shawarar sanya dokar ne don shawo kan rikicin.

KU KARANTA;Fasa taro: Shugaban APC Oshiomole ya rikirkita mahalarta bikn kaddamar da littafin Jonathan

Unguwannin da wannan dokar ta baci ya shafa sun hada da Yelwa Tsakani, Lushi, Unguwar Kusu, Unguwar Ngas da unguwar Kagadama, kamar yadda majiyar Legit.com ta ruwaito.

“A kokarinmu na tabbatar da tsaro da lafiyar mazauna unguwannin nan daga sharrin miyagun mutane da suke kokarin kara rura wannan rikici a jahar, gwamnati, gwamnati ta yanke shawarar sanya doka hana shige da fice daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe daga ranar Talata 20 ga watan Nuwamba.” Inji Gwamna Abubakar.

Sai dai Gwamna M.A ya bayyana cewa rikicin ya faro ne daga ranar Lahadi, 18 ga watan Nuwamba bayan wani rashin fahimta da aka samu tsakanin matasan unguwan Yelwa Tsakani da unguwar Lushi a yayin da ake yi tsaka da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar wata budurwa.

A sanadiyyar haka ne rikici ya kaure tsakaninsu, inda aka kashe mutane uku tare da barnata dukiyoyin jama’a, har ma da kona wasu gidaje guda biyu, har zuwa ranar Talata sai da wasu matasa suka yi fito na fito da jami’an rundunar Yansanda da aka tura don tabbatar da zaman lafiya.

Haka zalika wasu mata sun gudanar da zanga zanga dauke da ganyayyaki a hannuwansu don nuna bacin ransu a daidai lokacin da gwamnan jahar ya kai ziyarar gani da ido, inda matan suka nemi gwamnan ya sako musu matasan da aka kama.

Rahotanni sun tabbatar da cewa zuwa yanzu an kashe mutane uku, an jikkata mutane goma sha goma sha takwas, sa’annan Yansanda sun kama mutane saba’in da biyar dake da hannu a cikin rikicin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel