Tashin hankali: Yadda wani ‘Da’u fataken dare’ ya yi awon gaba da Mota daga ofishin Yansanda

Tashin hankali: Yadda wani ‘Da’u fataken dare’ ya yi awon gaba da Mota daga ofishin Yansanda

Rundunar Yansandan jahar Ondo ta shiga rudani biyo bayan satan wata babbar mota sukutum kirar Toyota Corolla da wani barawo yayi a wani daga ofisoshinta dake jahar Ondo, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito an kama motar ne a kwanakin baya, inda aka ajiyeta a harabar ofishin Yansanda na musamman dake yaki da garkuwa da mutane dake unguwar Alagbaka dake babban birnin jahar Ondo, Akure.

KU KARANTA: Karancin albashi: Gwamnoni sun garkame bakunansu bayan fitowa daga tattaunawa da Buhari

Baya da jibge motar a harabar ofishin kwararrun Yansanda, an cire batirin motar don gudun kada wani yayi gigin daukan motar, amma duk da haka sai gashi an samu wani sarkin iya shege ya yi awon gaba da motar, kuma har yanzu an kasa gano ko wanene.

Amma binciken farko farko ya tabbatar da cewa akwai dansanda dake aiki a ranar da aka sace wannan mota, kuma dansandan mai mukamin Sajan sabon zuwa ne, don kuwa ba’a dade da sauya masa wajen aiki ba zuwa ofishin.

Sai dai a yanzu haka an kama wannan Dansanda, an mikashi ga rundunar Yansanda ta musamman masu gudanar da binciken manyan laifuka dake garin Akure, inda ake cigaba da tsareshi tare da gudanar da bincike akan motar da aka sace.

Wata majiya ta karkashin kasa ta bayyana cewa: “Su kansu Yansandan dake aiki a wanna caji ofis sun shida rudani matuka da samun wannan labari, saboda an kama motarne aka ajiyeta a matsayin wata hujja inda har ta kai shiga kotu.

“A yanzu dai an gayyaci shugaban Yansandan ofishin zuwa babban ofishin Yansandan jahar don bayyana ma kwamishinan Yansandan jahar Gbenga Adeyanju yadda motar ta bace a karkashin sa idonsa.”

“Ya za’ayi ace barawo ya sadada cikin ofishin Yansanda, kwararrun Yansanda dauke da bindigu, har ya dauke mota” Kwamishinan ya tambaya, kamar yadda majiyarmu ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: