Wata budurwa ta yi asarar haihuwa bayan ta halaka dan jaririnta a Enugu

Wata budurwa ta yi asarar haihuwa bayan ta halaka dan jaririnta a Enugu

Rundunar Yansandan jahar Enugu ta kama wata budurwa mai shekaru ashirin da daya, 21, Sandra Chisom Dimbo bayan ta kashe dan jaririn data haifa, jim kadan bayan haihuwar tasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, Ebere Amaraizu ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace lamarin ya faru ne a wani babban otal dake garin Agbani na cikin karamar hukumar Nkanu ta yamma na jahar Enugu.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun halaka hadimin gwamna da Bom a jahar Kogi

“Hankulan jama’a ya tashi yayin da suka samu labarin uwa ta kashe danta a wannan Otal, uwar jaririn mai suna Sandra ta kashe jaririnta nata ne jim kadan bayan ta haifeshi a ranar 17 ga watan Nuwamba shekarar 2018.

“Sandra ta kashe jaririn ne a dakinta dake Otal din Royal, sai dai kukan jaririn yasa mutanen dake cikin dakunan dake makwabta da dakinta suka kutsa cikin dakin matar, inda suka kamata.” Inji Kaakakin.

Daga karshe kaakakin tace rundunarsu ta kaddamar da binciken kwakwaf don gano dalilin kashe jaririn, sa’annan tace tuni sun karbi gawar jaririn kuma sun mikashi ga dakin ajiyan gawarwaki.

Matsalar kashe jarirai dai ba yau farau ba, saboda an sha samun rahotannin dake bayyana yadda wasu iyaye mata marasa Imani suke kashe yayansu jarirai musamman wadanda suka samesu ta hanyar banza, watau cikin shege.

Kuma wannan matsala tayi kamari, matasala ce da ta zama ruwan dare, ba Musulmai ba, ba kirista ba, kowa na tafka wannan laifi, don kuwa ko kimanin watanni hudu da suka gabata sai da wata mata mai suna Aisha ta jefa jaririnta a karkashin motar tirela da nufin ta takashi a Kaduna.

Sai dai an ci sa’a hakan bai yiwu ba, inda aka ceto jaririn aka mika shi ga kwamishiniyar mata da cigaban al’umma ta jahar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, inda tace an ceto yaron ne a kusa da gadar sama ta Kawo, amma sun gano mahaifiyarsa na da tabin kwakwalwa, kuma tuni suka aika da ita asibiti, shi kuma yaron yana samun kulawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: