An kashe dan CJTF daya, sannan an sace mata yan gudun hijira 10 a wasu tagwayen hari da aka kai kauyukan Borno

An kashe dan CJTF daya, sannan an sace mata yan gudun hijira 10 a wasu tagwayen hari da aka kai kauyukan Borno

Yan ta’adan Boko Haram sun kashe wani dan tsaron sa kai wato civilian JTF guda sannan suka sace kimanin mata yan gudun hijira 10 daga gonakinsu a wasu tagwayen hare-hare da suka kai Borno.

Shugaban kauyen Mammanti, wani gari da ke Maiduguri, Mohammed Ibrahim Bulama ya fada ma majiyarmu ta Daily Trust cewa kimanin gidaje 100 ana cinna ma wuta yayinda yan ta’addan suka kwashe dabbobi da wasu kayayyakin amfani.

Sun ajiye kekunansu a kusa da wajen sannan suka fara harbi ba kakkautawa. Dukkaninmu mun bar gidajenmu da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba, sun sace mana shanaye sama da 120 da akuyoyi kafin su gona gidaje akalla 100.

An kashe dan CJTF daya, sannan an sace mata yan gudun hijira 10 a wasu tagwayen hari da aka kai kauyukan Borno
An kashe dan CJTF daya, sannan an sace mata yan gudun hijira 10 a wasu tagwayen hari da aka kai kauyukan Borno
Asali: Twitter

“Sun kuma kashe wani daga cikin yan tsaro na JTF mai suna Alhassa Kwali. Muna rokon gwamnati da ta kawo mana agaji, ko tabarma bamu das hi, ba abinci sannan sun lalata duk wani hanya da muke samu."

KU KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani ya yi wa gwamnoni wankin babban bargo akan mafi karanci albashi 30,000

Ya roki shugaban hafsan soji Laftanal Janar Buratai da ya tura sojoji kauyen saboda mutanensa na gudu saboda rashin tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel