Noman shinkafa: Najeriya ta rage shigo da shinkafa a Gwamnatin Buhari – Emefiele

Noman shinkafa: Najeriya ta rage shigo da shinkafa a Gwamnatin Buhari – Emefiele

Mun ji cewa Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Mista Godwin Emefiele ya karyata rahoton da ake yadawa na cewa yawan buhunan shinkafar da ake shigowa da ita a Najeriya ya karu da kusan 400, 000.

Noman shinkafa: Najeriya ta rage shigo da shinkafa a Gwamnatin Buhari – Emefiele
Noman shinkafa ya bunkasa a Gwamnatin Buhari inji CBN
Asali: Depositphotos

Godwin Emefiele yace labarin da ake ta zagayawa da shi na cewa shinkafar da aka shigo da ita Najeriya ya karu a shekarar nan. Gwamnan na babban banki yace babu gaskiya a rahoton da wasu Jaridun Kasar nan su ke yadawa.

Gwamnan yace abin da Najeriya ta shigo da shi na shinkafa bai wuce tan 25, 000 ba a kaf shekarar nan. Gwamnan na CBN ya bayyana wannan wajen wani babban taro da aka shirya na masana harkar tattalin arziki a Garin Legas.

KU KARANTA: Esther Okade: Karamar Yarinyar da ke neman yin Digiri na 3 a Ingila

Emefiele yayi karin bayani inda ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta kashe sama da Naira Biliyan 100 wajen harkar noman shinkafa da sauran hatsi a Najeriya. Emefiele yace Manoma fiye da 800, 000 sun amfana da tsarin.

A baya dai mun ji cewa Amurka tana harsashen Najeriya za ta shigo da buhuna fiye da 400, 000 na shinkafa a shekara mai zuwa. Hakan zai sa Najeriya ta zama Kasa ta 2 da ke kan gaba wajen shigo da shinkafa daga waje a Duniya.

Emefiele yace sam babu gaskiya harsashen da ake yi na cewa Najeriya ta bi sahun irin su Kasar China wajen shigo da kayan abinci. Emefiele yace yanzu CBN ta daina ba ‘Yan kasuwa Daloli wajen shigo da shinkafa cikin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel