Matasa 8 daga Najeriya sun shiga sahun matasan attajiran duniya na 2019

Matasa 8 daga Najeriya sun shiga sahun matasan attajiran duniya na 2019

Wasu matasa 8 'yan Najeriya na daga cikin matasan attajiran duniya na shekarar 2019, kamar yadda jaridar Forbes ta fitar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Forbes ta fitar da jerin sunayen matasan attajiran domin karfafa gwiwar 'yan kasuwa da ma su masana'antu kamar yadda ta saba yi kowacce shekara.

Matasan8 'yan Najeriya da sunan su ya bayyana cikin jerin attajiran matasa na duniya sun hada da, Taofeek Abijako, Kayode Ojo, Obi Omile Jr, Adegoke Olubusi, Tito Ovia, Dimeji Sofowora, Olaoluwa Osuntokun da Emmanuel Acho.

Taofeek Abijako, matashi mai shekaru 20, ya fara sana'ar dinka kayan maza tun yana makarantar sakandire.

Matasa 8 daga Najeriya sun shiga sahun matasan attajiran duniya na 2019
Taofeek Ajibako
Asali: Twitter

Kayode Ojo kuwa kwararren mai daukan hoto ne da yanzu haka ke da dakunan daukar hoto a birnin Paris na kasar Faransa, birnin Berlin na kasar Jamus, da biranen New York da Dallas a kasar Amurka.

Shi kuwa Obi Omile Jr, wata fasaha ya kirkira mai suna 'cut' da wanzaman zamani ke amfani da ita domin tsara yadda za su yiwa kwastomominsu aiki.

DUBA WANNAN: Babu wanda ya kama ni, karya ce kawai irin ta fadar shugaban kasa - Sanatan APC

Dimeji Sofowora da wasu ragowar mutane 26, sun kirkiri wata fasahar zamani ne da ke bawa likitoci a nahiyar Afrika damar samun bayanai daga marasa lafiya fiye 500,000.

Emmanuel Acho mai shekaru 28 ya kasance matashi ma fi karancin shekaru da ke sharhin labaran wasanni a gidan talabijin na ESPN, sannan yana da wani asibiti na taimakon ma su karamin karfi a Najeriya.

NAN ta rawaito cewar dukkan matasan ma su masana'antu ne da kuma wadanda su ka kirkiri wata fasaha da ke samar ma su da kudaden shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel