Abin kunya: Wata jami’a ta haramta ma daliban jahar Kano shiga aji a kasar Sudan
Daliban jahar Kano dake karatu a wata jami’ar kasar Sudan, Elrazi sun shiga mawuyacin hali bayan hukumar makarantar ta haramta musu shiga azuzuwa sakamakon rashin biyan kudin karatunsu da gwamnatin jahar ta ki biya.
Majiyar Legit.com ta ruwaito hukumar jami’ar El-Razi ta sanar da haka ne cikin wata wasika da aika ma gwamnatin jahar Kano a ranar 15 ga watan Oktoba, ta hannun hukumar bada tallafin karatu ta jahar Kano.
KU KARANTA: Kotu ta yanke ma yaron daya kashe babansa akan kudi a Bauchi hukuncin kisa
“Ya zama wajibi mu sanar daku cewa daga ranar 15 ga watan Oktoba ba zamu sake kyale dalibanku su shiga aji saboda baku biya musu kudin makaranta ba, kuma ku sani rashin shigarsu aji na tsawon wata daya ba zai basu damar kammala karatu a lokacin daya kamata ba.” Inji hukumar jami’ar.
Shima shugaban daliban jahar Kano dake karatu a Sudan, Saddiq Abdullahi Ubajalli ya tabbatar ma jaridar Daily Trust da wannan labari, inda yace suna neman agaji a cikin mawuyacin halin da suka fada, “Na rantse da Allah muna cikin matsanancin hali.” Inji shi.
“Jami’ar ta aika musu da takardun gargadi da dama kafin daukan wannan mataki, amma gwamnatin ba ta taba daukan mataki ba duk da gargadin da hukumar jami’ar ta yi musu, hakan ne yasa ta hana daliban shiga aji.
“Mu kanmu dalibai muna bin gwamnatin jahar kudin kashe na watanni 21, muna kuma binta bashin kudin wajen zama na watanni 11, a yanzu haka dalibai sun shiga mawuyacin hali.” Inji shi.
Ubajalli ya cigaba da bayyana cewa zuwa yanzu akwai dalibai mata guda goma da suka kammala karatun digiri tun awatan Agusta basu samu takardar shaidar kammala karatu ba saboda ba’a biya kudinsu ba.
Sai dai da yake martani, kwamishinan watsa labaru na jahar, Muhammad Garba ya musanta batun rashin biyan kudin makarantar daliban, amma ya tabbatar da daliban na binsu kudin daki da na kashewa, don haka yace gwamnatin jahar Kano za ta biya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng