NRHC za ta yi bincike game da kisan ‘Yan Shi’a daga 2014-2018 a Najeriya

NRHC za ta yi bincike game da kisan ‘Yan Shi’a daga 2014-2018 a Najeriya

Mun samu labari daga Vanguard cewa Hukumar kare hakkin Bil Adama watau NRHC ta bayyana cewa za ta binciki zargin kisan gillar da aka yi wa ‘Yan Shi’a kusan 500 a Najeriya shekaru 4 da su ka wuce.

NRHC za ta yi bincike game da kisan ‘Yan Shi’a daga 2014-2018 a Najeriya
Falana ya hurowa NRHC wuta ta binciki kisan da ake yi wa 'Yan Shia
Asali: Depositphotos

Hukumar ta NHRC ta tabbatar da cewa za ta duba zargin da ke kan Rundunar Sojojin Najeriya da kuma Jami’an ‘Yan Sandan kasar na kashe Mabiya addinin Shi’a babu gaira babu dalili da aka yi daga shekarar 2014 zuwa 2018 a cikin Najeriya.

NRHC ta tabbatar da hakan ne a wata wasika da ta aikawa babban Lauyan nan da ke kare hakkin Bil Adama watau Femi Falana. Falana ya aikawa Hukumar takarda kwanaki inda ya nemi ta binciki yadda Gwamnati ke tauyewa jama’a hakkin su.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta na neman ganin bayan Atiku da kulalliya – Inji Frank

Femi Falana SAN ya zargi Gwamnatin Tarayya da Buhari yake jagoranta da amfani da Jami’an tsaro wajen yi wa ‘Yan Shi’a kisan mummuke tare da hana su magana da yin addinin su da kuma fita tattaki da yin dandazo kamar yadda su ka saba.

Falana ya bayyana cewa an kashe Mabiya addinin Shi’a fiye da 492 a cikin shekaru 4 musamman a cikin Garin Zaria, Kaduna, Sokoto, Kano, da kuma Birnin Tarayya Abuja bayan daure Jagoran Kungiyar IMN Ibrahim Zakzaky da aka yi tun 2015.

Kwanan nan tsohon Gwamna Ayodele Peter Fayose ya soki Gwamnatin Buhari game da kashe 'Yan Shi'a a Kasar da aka yi a cikin Garin Abuja. Fayose yace bai dace a harbi ‘Yan Shi’a da ke fito-na-fito da Sojoji ba

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel