Biyu babu: An rasa sunan Tambuwal ciki sunayen 'yan takara da INEC ta saki
- Tambuwal na daga cikin 'yan takarar shugaban kasa da Atiku ya kayar a zaben fitar da 'yan takara na jam'iyyar PDP
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), reshen jihar Sokoto, ta ce babu sunan Tambuwal a cikin jerin sunayen 'yan takara da aka aiko daga Abuja
- Alhaji Mannir Dan Iya ne ya lashe tikitin yin takarar gwamnan jihar Sokoto a karkashin jam'iyyar PDP, a zaben fidda 'yan takara da aka yi a watan Satumba
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), reshen jihar Sokoto, ta ce babu sunan gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, a cikin jerin sunayen 'yan takara da aka aiko daga Abuja.
Malam Sadik Abubakar, kwamishinan hukumar INEC a jihar Sokoto ya shaidawa ya shaidawa gidan Radiyon BBC cewar PDP ta mika sunan Alhaji Mannir Dan Iya ne a matsayin dan takarar ta na gwamna a Sokoto.
Tambuwal na daga cikin 'yan takarar shugaban kasa da Atiku ya kayar a zaben fitar da 'yan takara na jam'iyyar PDP.

Asali: Twitter
Sai dai bayan kammala zaben, jam'iyyar PDP ta nemi ragowar 'yan takarar da Atiku ya kayar, su koma takarar kujerun kujerun da su ke kai.
DUBA WANNAN: Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna
Alhaji Dan Iya ne ya lashe tikitin yin takarar gwamnan jihar Sokoto a karkashin jam'iyyar PDP, a zaben fidda 'yan takara da aka yi a watan Satumba.
Kwamishinan zabe ya bayyana cewar jam'iyyar PDP na da nan zuwa 1 ga watan Disamba idan ta na da bukatar canja sunan dan takarar kujerar gwamna.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng