Babban malamin Kirista a Najeriya ya lissafan dalilan da ya sa musulunci ya fi Kiristanci

Babban malamin Kirista a Najeriya ya lissafan dalilan da ya sa musulunci ya fi Kiristanci

Wani babban malamin addinin kirista, Bishop Sam Zuga, da ke jagorantar wata coci 'house of oy' a Gboko da ke jihar Benuwe ya bayyana dalilinsa a kan cewar Musulmi sun fi kiristoci. Bishop Zuga ya bayyana hakan ne shafinsa na sada zumunta.

Malamin ya samu goyon bayan wani fitaccen kirista dan kudancin Najeriya, OAP Freeze, bayan an yi caa a kansa a kan kalaman da ya yi a matsayinsa na jagoran mabiya addinin Kirista.

Freeze ya kara da cewa; "da yawan musulmi sun fi kiristoci nuna halayen addinin Kirist, musamman balagurbin kiristoci irin na wannan zamani. Duk da ana samun rashin jituwa da kiyayya tsakanin Musulmi 'yan Shi'a da Sunni da kuma wasu balagurbin limamai, amma ba su kai sabbin darikun Kiritoci da ke kara bullowa ba."

Daga cikin dalilan da Bishop Zuga ya lissafa akwai batun cewar adadin mutanen da ke amsa suna Muhammed sun fi ma su amsa Emmanuel duk da kasancewar kiristanci ya fi Musulunci tsufa a duniya.

Babban malamin Kirista a Najeriya ya lissafan dalilan da ya sa musulunci ya fi Kiristanci

Babban malamin Kirista a Najeriya ya lissafan dalilan da ya sa musulunci ya fi Kiristanci
Source: Facebook

Kazalika ya bayyana cewar duk da an haifi annabi Muhammed shekaru 571 bayan mutuwar annabi Isa, Musulmi na goga kafada da Kiristoci ta fuskar yawan mabiya.

DUBA WANNAN: An kama malamin makarantar islamiyya da yiwa dalibar sa fyade

Bishop Zuga ya cigaba da cewa, "Qur'ani cikin harshe daya ya sauka amma za ka iya fassara shi zuwa kowanne harshen duniya amma akai littafin Injila (Bible) fiye da 10 cikin harshen Turanci kawai.

"Musulmi na yin sallah sau 5 a rana, Kiristoc na yin ibada sau daya a sati, wasu ko Cocin ma ba sa zuwa. Kuma duk inda Musulmi ya shiga, ragowar Musulmai za su karbe shi tare da nuna ma sa kauna."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel