Wani mai shekaru 95 da ya mutu ya dawo duniya

Wani mai shekaru 95 da ya mutu ya dawo duniya

Masu iya magana sukan ce duk wanda ke raye bai gama ganin abin al'ajabi ba. Wani dattijo mai shekaru 95 dan kasar Indiya ne ya rasu bayan ya suma a yankin Arewa maso Yammacin Rajasthan har likita ya tabbatar da mutuwarsa. Hakan yasa 'yan uwansa suka fara shirye-shiryen jana'izarsa.

Sai dai a yayin da aka fara shirin birne shi mutumin mai suna Budh Ram kwatsam sai ya farka wadda hakan ya razana mutane. Baban dansa mai suna Balu Ram ne ke yi masa wanka sai ya lura mahaifinsa ya fara shure-shure.

Ya kara da cewa mahaifinsa ya farka ne bayan ya zuba masa ruwa a kirji yayin da ya ke masa wankan. Dan nasa mai shekaru 65 ya bayyana cewa wani wata mu'ujiza ne daga ubangiji.

Wani mai shekaru 95 da ya mutu ya dawo duniya

Wani mai shekaru 95 da ya mutu ya dawo duniya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan irin tarbar da aka yiwa Buhari yayin da ya isa Paris

Kalamansa: "Ya fara numfashi sannan ya tashi ya zauna kan gado. Da aka masa tambaya, ya fada musu cewar kirjinsa ne ke masa ciwo hakan yasa ya yi barci. Wannan dai al'amari ne mai ban al'ajabi."

Wani daga cikin 'ya'yansa mai suna Ranjit Ram ya bayyana cewa wannan abin farin ciki ne ga iyalan dattijon. Dan nasa mai shekaru 55 ya ce: "Za muyi bukin Diwali cikin annashuwa. Idan da ace mahaifinmu ya rasu ba za muyi shagulgulan ba saboda zaman makoki amma wannan karon shagulgulan za su bunkasa."

A baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewa wani fasto mai ya farfado bayan likitoci sun tabbatar da mutuwarsa. Faston mai suna Anderson Chinenye ya farfado ne bayan an kai shi dakin ajiye gawa wato mortuary.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel