Muna ta nazarin yadda za mu fara biyan sabon tsarin albashi - Wabi gwamnan APC a Arewa

Muna ta nazarin yadda za mu fara biyan sabon tsarin albashi - Wabi gwamnan APC a Arewa

Gwamnan Jijhar Neja Abubakar Sani Bello yace yana nazari akan sabon tsarin albashi na naira dubu 30 da aka cimma yarjejeniya a tsakanin kungiyar kwadagon Nigeria da kuma gwamnatin Kasar.

A hira da manema Labarai a harabar majalisar dokokin jihar, gwamna Abubakar sani Bello yace abinda zasu iya yi shine zasu biya domin aikin gwamnati yana da yawa.

Muna ta nazarin yadda za mu fara biyan sabon tsarin albashi - Wabi gwamnan APC a Arewa

Muna ta nazarin yadda za mu fara biyan sabon tsarin albashi - Wabi gwamnan APC a Arewa
Source: Depositphotos

Legit.ng Hausa ta tsinkaye she yana cewa akwai ayyukan ci gaban sauran Jama ‘a kamar samar da ruwa, asibiti da dai sauransu.

Yace dangane da batun karin albashi jihar Naija ta riga ta tsaida wannan shawarar tana jira ne kawai taji matsayin gwamnatin tarayya kafin ta fara aiwatarwa.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Gombe dake a Arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar cafke wani malamin Islamiyya mai suna Raudatul Qur’an mai shekaru 26 a duniya da laifin yiwa dalibar sa mai shekaru 5 fyade a ofishin sa.

Jami'an 'yan sandan yayin da suke nunawa manema labarai malamin mai suna Bilyaminu Halilu, tare da sauran masu laifin da suka kama sun bayyana cewa sun cafke shi ne a ranar 1 ga watan Oktoban da ya gabata a garin Gona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel