Yajin aiki: ASUU ta bayyana abinda ta ke bukata daga gwamnatin tarayya

Yajin aiki: ASUU ta bayyana abinda ta ke bukata daga gwamnatin tarayya

- Shugaban ASUU na kasa, Abiodun Ogunyemi ya yi magana kan yajin aikin da kungiyar ta shiga cikin kwana-kwanan nan

- A ranar Lahadi 4 ga watan Nuwamba ne ASUU ta sanar da cewar za ta fara gudanar da yajin aiki na gama gari

- Kungiyar ta na zargin gwamnatin tarayya da rashin cika alkawurran biyan N1.1 triliyan da ta dauka wa kungiyar na tsawon shekaru

Shugaban kungiyar malaman jami'o'in Najeriya na kasa (ASUU) Abiodun Ogunyemi ya bayyana cewa kungiyar ba za ta dage yajin aikin da ta fara ba har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu.

Kungiyar tana zargin gwamnatin tarayya da rashin cika alkawurran da ke cikin yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar da gwamnati suka rattaba hannu a kai tun a shekarar 2013.

ASUU ta bayyana abinda ta ke bukata daga gwamnatin tarayya
ASUU ta bayyana abinda ta ke bukata daga gwamnatin tarayya
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Shekau ya mayar da martani ga wadanda suka ce ya mutu (Bidiyo)

Ogunyemi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Nigerian Tribune inda ya ce gwamnatin ta bawa kungiyar N200 biliyan ne kawai a tsakanin 2013 zuwa 2017. Ya ce kungiyar na jiran cikin N1.1 triliyan daga gwamnatin tarayya.

A cewarsa, "Ya kamata gwamnati ta saki kudaden ne tun Oktoban shekarar 2017 kamar yadda ya ke a yarjejeniyar da ASUU da gwamnatin suka sanya hannu a kai.

"A cikin yarjejeniyar, gwamnati ta amince za ta samar da kudade domin inganta jami'o'in da ke kasar domin farfado da ilimi. Jimlar kudin shine N1.3 tiriliyan wanda ya kamata a bia daga 2013 zuwa 2017 amma N200 biliyan kawai aka biya sauran N1.1 tiriliyan.

"Da ASUU ta tuntube gwamnati a bara kan batun biyan kudi, gwamnatin ta bayyana cewa bata manta ba inda suka bayar da N20 biliyan sannan su kace za su cigaba da duba yadda za a biya sauran kudaden.

"Gwamnatin ta kafa kwamitin mutane 7 da za ta nemo hanyoyin da za a samo kudin kuma sunyi aikinsu su bayar da rahoto wanda aka ajiye a yana shan kura. Muna tsamanin gwamnati ta rika biyan N220 biliyan duk shekara ne ta yadda za su biya dukkan kudin cikin shekaru biyar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel