An dage shari’ar Gwamnati da Ekweremadu sai shekara mai zuwa

An dage shari’ar Gwamnati da Ekweremadu sai shekara mai zuwa

- Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da rokon Gwamnatin Tarayya na damke Ike Ekweremadu

- Gwamnatin Najeriya ta nemi ayi ram da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan amma Kotu tayi watsi da batun

- Ana tuhumar Shugaban Majalisar Dattawan Kasar da kin gabatarwa Hukumar kasa da duk kadarorin da ya mallaka

An dage shari’ar Gwamnati da Ekweremadu sai shekara mai zuwa

Sai 2019 za a cigaba da shari’ar Sanata Ike Ekweremadu
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa babban Kotun Tarayyar Najeriya da ke zama a Birnin Tarayya Abuja ba tayi na’am da rokon da Gwamnati tayi na tsare Sanata Ike Ekweremadu a shari’ar da ake yi game da kadararorin da Sanatan ya mallaka ba.

Sanata Ike Ekweremadu ya ki hallara gaban Kotu inda ake shari’a da shi da Gwamnati kwanaki wanda hakan ya sa Lauyan Gwamnatin Tarayya watau Celcus Ukpong ya nemi Kotu tayi amfani da karfin ta, ta sa a kama babban Sanatan.

A jiya Alhamis ne aka koma gaban Kotu inda ake shari’a tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekeremadu inda ake zargin cewa bai bayyanawa Hukuma wasu kadarorin sa ba.

KU KARANTA: Ban da masaniyar cewa gidan Ekweremadu mu ka je fashi – Inji Barawon da aka kama

Alkali Mai shari’a Binta Nyako ba ta gamsu da rokon da Lauya Celcus Ukpong yayi ba har sai an warware sarkakiyar shari’ar a Kotun daukaka kara. Alkalin tace ba za ta nemi a kamo Sanatan ba har sai an binciki hurumin Kotun ta a shari’ar.

Tuni dai babban Lauyan da ke kare Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan watay Adegboyega Awomolo (SAN) ya nemi Kotu tayi watsi da abin da Gwamnati ta ke nema. Yanzu dai an dage shari’ar har sai zuwa karshen Watan Fabrairun 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel