Malam Mai Rakumi zai sha daurin shekaru 10 a gidan yari

Malam Mai Rakumi zai sha daurin shekaru 10 a gidan yari

Labari ya zo mana daga Jaridar nan ta Daily Trust cewa Babban Kotun Tarayyar Najeriya da ke cikin Garin Kano ta yankewa wani babban Malamin da aka sani mai aiki da rauhanai hukuncin dauri a gidan kurkuku.

Malam Mai Rakumi zai sha daurin shekaru 10 a gidan yari

Kotu ta daure wani babban Malami mai aiki da rauhanai a Kano
Source: Twitter

Malam Abubakar Isaq wanda aka fi sani a Gari da Mai-Rakumi zai yi zaman gidan yari na tsawon shekaru 10 bayan an same shi da laifin mallakar kudin jabu. Alkali Lewis Allagoa ne dai ya sami Malamin da duka laifin da ake tuhumar sa.

Alkali mai shari’a ya tabbatar da cewa Malam Mai Rakumi ya aikata laifuka 2 da ake zargin sa da su na mallakar makudan kudi na jabu. Kwanaki ne Hukumar nan ta EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta damke sa.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Kwankwaso zai yi sallar juma'a a cikin Kano

EFCC ta kama Malamin tsibbun ne bayan Hukumar NDLEA ta yi ram da shi da laifin shigowa da makudan kudi na Daloli amma na jabu. A dalilin haka ne aka maka shi a Kotu har ta kai Lauyan sa ya karbo belin sa ba da dadewa ba.

A jiya Kotu ta kama Malamin da laifi inda ta yanke masa shekaru 10 a gidan yari bayan ya furta da bakin sa cewa ya aikata laifukan da ake zargi. Lauyan da yake kare Malamin watau Barista Mohammed Aliyu ya nemi ayi masa rangwame.

Mohammed Aliyu ya nemi a maidawa Malamin hukuncin daurin zuwa tara amma Mai shari’a Allagoa ya ki amincewa da hakan. Alkalin ya kuma nemi a lalata kudin jabun da aka samu wajen babban Malamin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel