Badakalar Ganduje: Mutumin daya fallasa bidiyon karbar cin hanci ya amince ya bayyana gaban majalisa

Badakalar Ganduje: Mutumin daya fallasa bidiyon karbar cin hanci ya amince ya bayyana gaban majalisa

Dan kwangilar daya baiwa gwamnan jahar Kano Abdullahi Umae Ganduje tare daukansa bidiyoya bayyana cewa a shirye yake ya gurfana gaban majalisar dokokin jahar Kano don zube musu hujjjojinsa game da sahihancin wannan bidiyo.

Majiyar Legit.com ta ruwaito dan kwangilar da bai bayyana sunansa ba ya bayyana ma majalisar burinsa na gurfana a gabansu ne cikin wata wasika da lauyansa Saeed Twada ya kai ma majalisar kafa da kafa, inda yace shi ne ya dauki Ganduje hoton, don haka yace akwai bukatar Ganduje ma ya bayyana.

KU KARANTA: Bani da masaniyar cewa gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa muka je fashi ba – Barawo

Idan za’a tuna jaridar Daily Nigerian ce ta fara wallafa bidiyon Ganduje yayin da yake karbar cin hancin makudan kudade da suka haura dala miliyan biyar daga hannun dan kwangila a shafinta na yana gizo.

Sai dai tun bayan bayyanar wannan bidiyo ne sai majalisar dokokin jahar Kano ta kafa wata kwamitin mutane bakwai da ta daura mata nauyin gudanar da cikakken bincike akan lamarin domin tabbatar da gaskiyar bidiyon ko akasin haka.

Amma fa wani hanzari ba gudu ba, tunda wannan kwangila da yayi alkawarin bayyana gaban majalisar ya gindaya wasu sharudda wanda zai an cikasu zai samu damar bayyana a gaban yayan majalisar ta dokokin jahar Kano, sharuddan sune;

- Za’a baiwa kwararrun masu bincike guda biyu fafyan bidiyon domin su tabbatar da sahihancinsa

- Dole ne guda daga cikin masu binciken ya kasance jami’in hukumar DSS da dan kasan waje, kuma jahar ce za ta biya kudin aikin.

- Za’a mika masa rahoton binciken da kwararrun suka yi kafin ya bayyana gaban majalisar

- Ya yarda zai mika dukkanin na’urorin da yayi amfani dasu wajen daukan bidiyon gaba daya

- Za’a mika masa dukkanin tambayoyin da majalisar za ta yi masa, kuma ba zasu wuce goma ba

- Dole ne a iyakance mutanen da zasu halarci zaman sauraron da zai gudana a majalisar

- Za’a kyale dan kwangilar ya sanya fuskar badda kamanni tare da amfani da sunan karya don kare kansa, iyalansa da kasuwancinsa.

- Dole ne sai gwamnan jahar Kano, dan jarida Jaafar Jaafar da shugaban Hisbah Malam Aminu Daurawa sun halarci zaman.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel