2019: Gwamnonin APC da Ministoci na neman jikawa Oshiomhole aiki

2019: Gwamnonin APC da Ministoci na neman jikawa Oshiomhole aiki

Mun samu labari daga Jaridar Vanguard cewa Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole yana ganin ta-kan sa inda yanzu har ta kai wasu Gwamnoni 4 su na shirya masa wata makarkashiya a cikin Jam’iyyar.

2019: Gwamnonin APC da Ministoci na neman jikawa Oshiomhole aiki

Gwamnonin Jihohi sun fara kitsawa Shugaban APC danyen aiki
Source: Depositphotos

Wasu daga cikin Gwamnonin Jihohi na Jam’iyyar APC sun fara neman hadin-kan Ministoci domin ganin Oshiomhole ya bar mukamin sa na Shugaban Jam’iyyar APC na kasa saboda ya hana su yadda su ke so a game da zaben 2019.

Gwamnonin na APC su na neman Ministoci su taya su yakar Adams Oshiomhole ne a sakamakon abin da ya faru a zabukan fitar da gwani da aka yi a Jam’iyyar inda wasu Gwamnonin Jihohi su ka gaza ba wadanda su ke so tikitin takara.

Kamar yadda mu ka ji, Gwamnonin su na kukan cewa Adams Oshiomhole kadai yayi yadda yake so a Jam’iyyar inda ya hana Gwamnonin taka wata rawa wajen kakaba Magadan su ko kuma nemawa Mutanen su a kujerar Majalisa.

KU KARANTA: Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya

Wani Gwamna yayi kaca-kaca da Shugaban Jam’iyyar inda yace har gobe babu wanda ya isa yayi takara a Jihar Edo sai tsohon Gwamna Adams Oshiomhole ya dafa masa amma kuma ya hana Gwamnonin da ke APC yanzu yin abin da su ke so.

Ana dai zargin Adams Oshiomhole da nada Magajin sa Godwin Obaseki da karfi da yaji a Jihar sa amma kuma duk da wannan ya hana wasu Gwamnonin APC mika tikiti ga wadanda su ke so don haka su ke naman a tsige sa daga kujerar sa.

Haka kuma Gwamnonin su na jin haushin Asiwaju Bola Tinubu wanda jigo ne a Jam’iyyar a dalilin goyon bayan Shugaban APC na kasa da yake yi. Wasu a Jam’iyyar dai sun nemi Tinubu ya janye goyon bayan da yake ba Adams Oshimhole.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel