2019: ‘Dakikan Shugabanni aka samu su ke mulkin Najeriya – ‘Dan takaran AAC Sowore

2019: ‘Dakikan Shugabanni aka samu su ke mulkin Najeriya – ‘Dan takaran AAC Sowore

‘Dan takarar Shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar AAC ta ‘African Action Congress’ watau Omoyele Sowore yayi alkawarin daure Barayin kasar nan idan har ya samu mulki.

2019: ‘Dakikan Shugabanni aka samu su ke mulkin Najeriya – ‘Dan takaran AAC Sowore
Sowore yace zai daure su IBB ya inganta noman wiwi ya kuma kara albashi
Asali: UGC

Yele Sowore ya bayyana cewa zai kama tsofaffin Shugaban kasar nan irin su Olusegun Obasanjo da su Ibrahim Babangida idan har ya samu mulki. Sowore yace ko da karshen kwanan su ya zo, zai daure su idan har ya samu iko.

‘Dan takarar Shugaban kasar ya caccaki tsofaffin Shugabannin Kasar wadanda ya kira mutanen Banza kamar yadda mu ka samu labari. ‘Dan takarar ya kuma ce tsofaffin Shugabannin da su ka mulki Najeriya sam ba su da tunani.

KU KARANTA: 2019: ‘Yan takara fiye da 100 sun kai karar Adams Oshiomhole gaban Kotu

‘Dan takarar yace yana kuma nan a kan bakar sa na ganin ana samu kudin shiga ta hanyar fita da tabar wiwi wajen Najeriya domin kuwa irin ganyen wiwin da ake nomawa a Najeriya yana da kyau ko da ba zai halatta shan tabar ba.

Sowore wanda shi ne Mai gidan Jaridar nan ta Sahara Reporters da ke Kasar Amurka ya kuma soki Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai shekaru 76 wanda har yanzu ake zargin bai da takardar shaidar jarrabawar sa ta WAEC.

Matashin ‘Dan takarar yace idan har za a karbo kudin da Marigayi Janar Sani Abacha ya sace, dole a bankado irin makudan kudin da su Cif Olusegun Obasanjo su ka sace. ‘Dan takarar ya kuma ce dole a karawa Ma’ikatan kasar nan albashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel