Kaico! Yadda fada tsakanin wasu abokai akan kudi N400 ya kazanta

Kaico! Yadda fada tsakanin wasu abokai akan kudi N400 ya kazanta

Rundunar Yansandan jahar Legas ta yi ram da wani matashi mai shekaru 25, Morenikeji Oguntoyibo da laifin fasa kwalba tare da caka ma wani abokinsa Emmanuel Ibeh a wuya a daidai lokacin da rikici ya kaure a tsakaninsu, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar 26 ga watan Oktoba, yayin da fada ya kaure tsakanin abokan biyu a gidansu dake tashar mota ta Benson a unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

KU KARANTA: Take hakkokin bil adama: Majalisar dinkin Duniya ta fara binciken kasashe 14, har da Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa rikici ya kunno kai ne bayan Ibeh ya baiwa Moreni kudi naira dari hudu (N400) ya ajiye masa, amma bayan kimanin awa daya da ya nemi kudinsa, sai Moreni yace masa ya kashe kudin a caca, kuma bai ciyo komai ba.

Daga nan ne Ibeh ya harzuka, inda ya kai ma Moreni naushi, shi kuma ganin haka ya sauka kasa, inda ya dauko kwalba, ya fasata ya nufi Ibeh da gudu, isarsa kansa keda wuya ya caka masa a wuya, kafin a ankara jini ya fara kwarara.

Dansanda mai shigar da kara, Sajan Mary Ajitery gurfanar da Moreni gaban Alkalin wata kotun majistri dake Ikorodu, Candide Johnson, wanda shine yake sauraron karar, inda ta bayyana masa cewa Moreni ya raunata Ibeh sosai ba kadan ba, don kwua har yanzu baya cikin hayyacinsa.

Tsananin yankan ta sanya sai da aka mika shi ga manyan asibitoci har guda uku, sa’annan aka garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar jahar Legas, inda daga nan suka bada shawarar a karasa da shi zuwa babban asibitin koyarwa na garin Ibadan.

Sajan Mary ta cigaba da bayyana ma Kotun cewa ana tuhumar Moreni da laifin kokarin aikata kisan kai, sanya rayuwar dan adam cikin hatsari, cutar da dan adam, wanda dukkaninsu sun saba ma sashi na 230, da na 245 na kundin hukunta manyan laifuka. Sai dai Moreni ya musanta aikata laifukan gaba daya.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin sai Alkalin kotun, W.B Balogun ya bada belin wanda ake kara akan kudi naira miliyan daya, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, wanda dole sai sun kasance yan uwansa ne, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: