Atiku da Buhari sun raba kan jaruman Kannywood

Atiku da Buhari sun raba kan jaruman Kannywood

- A yayin da siyasa ke cigaba da mamaya da ratsa jiki da harkokin jama'a, an yi sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman Kannywood

- Yin sharhin ya biyo bayan ganin yadda jaruman ke fitowa fili domin nuna goyon bayansu ga dan takarar da su ke ra'ayi

- Sai dai har yanzu ba a san ina fitaccen jarumi Ali Nuhu ya saka gaba ba

Sannu a hankali siyasa sai kara shiga duk sabgogi da kasuwancin jama'a ta ke yi. Irin wannan mamaya da siyasa ke yi ne ya saka sashen watsa labarai na BBC Hausa ya yi wani sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Yin sharhin ya biyo bayan ganin yadda jaruman ke fitowa fili domin nuna goyon bayansu ga dan takarar da su ke ra'ayi.

Atiku da Buhari sun raba kan jaruman Kannywood
Ziyarar wasu jaruman Kannywood ga shugaba Buhari
Asali: Twitter

Ko a kwanakin baya sai da legit.ng ta kawo ma ku labarin wasu jaruman masana'antar Kannywood da su ka kai ziyara fadar shugaba Buhari.

A yayin da jarumai irinsu Adam A. Zango, Darekta Aminu Saira, Rikadawa, Daushe, Fati Shu'uma, Rukayya Dawayya da wasu da dama ke goyon bayan takarar Buhari, jarumai irinsu Sani Danja, Bashir Nayaya, Fati Muhammad, da sauransu cewa su kai sai Atiku.

DUBA WANNAN: Ka zo mu baka nasara a zaben 2019 - Guru Maharaji ya fadawab Buhari

Sai dai har yanzu ba a san ina fitaccen jarumi Ali Nuhu ya saka gaba ba.

Sai dai da yawa na ganin cewar jaruman masana'antar ta Kannywood da ta hada har da ma mawaka, sun fi karkata bangaren gwamnati, ma su goyon bayan APC da takarar shugaba Buhari sun fi yawa.

Mawakan da ake yayi irin su Adamu Gwanja, Rarara, da sauransu na tare ne da shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel