An kama tsohon ‘Dan wasan kasar Italiya Iaquinta dauke da bindigogi

An kama tsohon ‘Dan wasan kasar Italiya Iaquinta dauke da bindigogi

- Kotu ta yankewa Vincenzo Iaquinta daurin shekaru 2 a gidan yari

- Ana kama tsohon ‘Dan wasan gaban na Juventus dauke da bindiga

- Kotu ta kuma yankewa Mahaifin sa Giuseppe daurin shekaru har 19

Mun samu labari cewa Kotu ta kama tsohon ‘Dan wasan kasar Italiya Vicente Iaquinta da laifin rike bindigogi. Wannan laifi dai ya sabawa dokar kasar kuma za a iya daure sa har na tsawon shekaru biyu idan an gama shari’a.

Ana zargin tsohon ‘Dan wasan gaban na Juventus da daurewa wasu ‘Yan daba gindi ta hanyar mallakar wasu kananan bindigogi kirar Magnum revolver da harsashi sama da 120 a lokacin yana bugawa Kungiyar Juventus wasa.

An kama tsohon ‘Dan kwallon ne a karshen 2015 inda aka soma shari’a. Yanzu dai an same sa da laifi inda ya bayyanawa Kotu cewa ya ajiye bindigogi ne domin ya koyi harbi don ya kare kan sa a nan gaba saboda sharara da yayi.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar Zidane ya maye gurbin Mourinho a Man United

An binciki ‘Dan wasan kwallon kafan ne tare da wasu mutane sama da 140 a Garin Calabria da ke Kudancin Kasar Italiya. Kotu ta samu Iaqunita da laifin hada-kai da gungun ‘Yan daban da ake kira Ndrangheta da su addabi jama’a.

Mahaifin ‘Dan wasan mai suna Giuseppe wanda aka haramtawa rike makami zai fuskanci wa’adin shekaru 19 a gidan yari bayan an same sa da laifi. Yanzu dai Iaqunita da tsohon na sa su na da damar daukaka kara kafin a daure su.

‘Dan wasan gaban na Jueventus da ya taba cin kofin Gasar Duniya da kasar sa Italiya a 2006 ya sha da kyar ne inda aka nemi Alkali mai shari’a ya yanka masa daurin akalla shekaru 6 a gidan kurkuku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel