Kwan gaba kwan baya: Najeriya ta rikito daga jerin kasashen da suka fi saukin hada hadar kasuwanci
Najeriya ta rikito zuwa kasan kasa a karo na farko daga jerin kasashen Duniya dake da saukin gudanar da kasuwanci a Duniya, kamar yadda alkalumma daga rahoton bankin duniya suka bayyana, inji rahoton jaridar The Cables.
Majiyar Legit.com ta ruwaito bankin ta fitar da wannan rahoto ne a ranar Laraba 31 ga watan Oktoba, da taken, ‘Kasuwanci a shekarar 2019: Shekarar garambawul da daukaka.’, inda tace Najeriya ta rikito daga matsayinta na baya.
KU KARANTA: Likafa ta ci gaba: Tsohon kaakakin Goodluck Jonathan ya samu tikitin takarar mataimakin gwamna
A shekarun 2017 da 2016, Najeriya kasa ta 145 da 169 a jerin kasashen duniya da suka fi sauki ga yan kasuwa su kulla kasuwanci da cinikayya, amma sai gashi a shekarar 2018 Najeriya ta koma kasa ta 146, inda kasar Mali ta tunkudeta daga tsohon matsayinta.
Rahoton bankin duniyan ya bayyana cewa ya gano garambawul guda 314 da gwamnatocin kasashen duniya 128 suka samar don inganta cinikayya.
” Gwamanatoci na da babban aiki a gabansu na samar da ingantaccen yanayin gudanar da kasuwanci, inda kanana da matsakaitan yan kasuwa zasu ji dadi.” Inji shugaban bankin, JimYong Kim.
Kim ya cigaba da fadin: “Sahihan dokokin dake tafiyar da kasuwanci na da matukar muhimmanci wajen habbaka fannin yan kasuwa masu zaman kansu, idan ba’a tanajesu ba kuwa, ba zamu taba ganin karshen talauci ba a duniya gabaya.”
Rahoton ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta samar da gyare gyare guda hudu game da saukaka kasuwanci a kasar, daga ciki akwai saukaka kasuwanci a jihohin Kano da Legas, ta hanyar fadada wutar lantarki a jihohin da kuma kara hada hadar kasuwanci a tsakanin jihohin biyu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng