Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya ta yi watsi da bukatar gwamnoni akan karancin albashi

Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya ta yi watsi da bukatar gwamnoni akan karancin albashi

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa bata da amince da tayin naira dubu ashirin da biyu da dari biyar (N22, 500) da gwamnonin jihohin Najeriya suka yi ma kungiyar kwadago tayi a matsayin karancin albashi ba, kamar yadda ministan kwadago, Chris Ngige ya bayyana.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Chris Ngige ya bayyana haka ne a ranar Laraba cikin wata hirar wayar tarho da yayi da gidan talabijin na Channels a shirin safe, inda yace kudin da gwamnonin suka yanke bai isa ba, ya yi kadan.

KU KARANTA: Kun barmu cikin mawuyacin hali – Sojojin Najeriya sun mayar ma Ministan Buhari martani

“Babu abinda gwamnoni suka yi a haka, na fada musu gwamnatin tarayya bata amince da wannan kudi na N22,500 ba. saboda bai ma kai N24,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi ba.” inji shi.

Sai dai yace yana kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a tattaunawar da ake yi game da karancin albashi dasu koma kan teburin tattaunawa don ganin an cimma matsaya game da walwalar ma’aikata.

“Karancin albashi a kasa doka ce wanda gwamnatin tarayya take bibiya, kamar yadda yake a lamba ta 34 a jerin kudurorin da gwamnati ta mika ma majalisa, amma bai kamata ayi dokar da mutane zasu karyata tun da fari ba.

“Idan ka yi doka da alkalumma marasa tabbas, wanda ba’a amince mas aba, kuma wanda mutane basu da halin biya, musamman saboda dokar kwadago ta kasa ta dage lallaai har sai idan kasa za ta iya biya.” Inji shi.

Daga karshe Ngige ya bayyana damuwarsa da nukusanin shugaban kwamitin tattaunawar, Amal Pepple, wanda yace ta tafi kasar waje domin a duba lafiyarta, amma duk da bata nan, yace zasu gayyaci sauran yayan kwamitin don cigaba da tattaunawa.

Idan za’a tuna a ranar Laraba ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdul Azeez Yari ya bayyana cewa gwamnoni sun yanke shawarar biyan N22, 500 a matsayin karancin albashi, inda yace sun yanke haka ne saboda halin da ake ciki.

A bangare guda kuma, kungiyar kwadago ta dage kai da fata akan lallai ba za ta amshi duk abinda ya yi kasa da naira dubu talatin (N30,000) a matsayin sabon karancin albashi ba, inda ta yi barazanar shiga yajin aikin dindindin daga ranar 6 ga watan gobe idan ba’a cika mata ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng