Gyadar doguwa: Da na zauna a APC da kashi na ya bushe kamar Gwamnan Ogun - Saraki

Gyadar doguwa: Da na zauna a APC da kashi na ya bushe kamar Gwamnan Ogun - Saraki

Mun samu labari daga Jaridar This Day cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yayi magana game da abin da ke faruwa da irin su Gwamnan Jihar Ogun Ibekunle Amosun a Jam’iyyar APC mai mulki.

Gyadar doguwa: Da na zauna a APC da kashi na ya bushe kamar Gwamnan Ogun - Saraki
Saraki yace APC ta wulakanta Amosun duk da kusancin sa da Buhari
Asali: Depositphotos

Bukola Saraki yace irin abin da yake faruwa da Gwamna Amosun yanzu ya sa tun farko ya tsere daga Jam’iyyar APC. Saraki yace bai dai so yayi wa APC katsalandan amma abin da aka yi wa Gwamna Ibekunle Amosun sam bai dace ba.

Bukola Saraki ya kuma bayyana cewa Gwamnan na Jihar Ogun yana cikin manyan Aminan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin Jam’iyyar APC. Saraki yace a lokacin da Shugaban kasar bai da lafiya Amosun ya fi kowa damuwa.

KU KARANTA: Yadda za ni Magance rashawa idan na tika Buhari da Kasa - Mimiko

Shugaban Majalisar Dattawa yace a lokacin da Buhari ba ya Najeriya, Gwamna Amosun ne kadai bini-bini ya kan tuntubi Majalisa domin ya ji inda kasar ta sa gaba. Saraki yace a lokacin duk ‘Yan APC babu wanda ya kara bi ta kan Buhari.

Saraki yace bai taba tunanin Jam’iyyar APC za tayi wa Amosun abin da tayi masa ba inda yace irin abin da ya hango kenan ya tsere daga Jam’iyyar tun kafin 2019. Saraki yace da ya tsaya a APC da ko fam din takaran zabe ba za a saida masa ba.

Sanatan ya kuma bayyana cewa alkaluma sun nuna Alhaji Atiku Abubakar ne zai yi nasara da aka yi masa tambaya game da zaben 2019, sai dai yace ba za su cika baki ba har sai lokacin yayi tukuna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel