Cikin Hotuna: Tattakin da Kungiyar Shi'a ta fara gudanarwa a jihar Kano
A jiya Alhamis kungiyar nan ta IMN da ta fi shahara da sunan Shi'a, ta fara gudanar da tattakinta na makoki Arba'in kamar yadda ta saba a kowace shekara daga birnin Kano zuwa cibiyarta ta Hussainiya dake garin Zaria a jihar Kaduna.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar 'yan sandan jihar Kano ta tari numfashin kungiyar inda ta yi gaggawa hana ta gudanar da wannan tattaki bisa dalilai na gudun kawo cuzguni da takura ga al'umma a sanadiyar tattakin da zai gudana a manyan hanyoyi dake Kanon ta Dabo musamman yankin Gadar Lado dake unguwar Gyadi-Gyadi da zamto mashiga da mafita ta jihar.
KARANTA KUMA: Wani 'Dan Majalisar Wakilai na jihar Akwa Ibom ya fice daga jam'iyyar PDP
A baya kungiyar da sanadin kakakin ta, Dakta Dauda Nalado, ta nemi alfarmar hukumar 'yan sanda da kuma gwamnatin jihar Kano wajen neman hadin kansu yayin tattakin da za ta gudanar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng