Wayyo! An yi kare jini, biri jini a wata karanbatta tsakanin yan daba da Yansanda a Kano

Wayyo! An yi kare jini, biri jini a wata karanbatta tsakanin yan daba da Yansanda a Kano

Wasu gungun yan daba ko a ce musu yan sara suka sun kashe jami’in Dansanda a wata karanbatta da aka yi a lokacin da jami’an Yansanda suka far musu a unguwar kwanar jaba dake cikin karamar hukumar Nassarawa ta jahar Kano, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito wannan rikici ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata, sai dai majiyar tace akwai wani dan daba guda daya da Yansanda suka kashe a yayin wannan arangama.

KU KARANTA: Wani Sanata daga babbar jahar PDP ya yi wankan tsarki ya fada jam’iyyar APC

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Magaji Musa Majia ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Laraba 24 ga watan Oktoba, inda yace lamarin ya faru ne a lokacin da Yansandan ke sintirin lunguna da mabuyar yan miyagun mutane.

A cewar SP Majia, rundunar Yansandan jahar Kano ta samu bayanai ne daga wasu mutane mazauna unguwar kwanar Jaba game da wata mabuyar miyagun mutane dake unguwarsu, nan da nan aka aika da rundunar Yansanda ta musamman dake yaki da ayyukan dabanci don ta kamasu.

“Isar Yansanda keda wuya sai suka kama yan daba guda 4, amma akan hanyarsu ta komawa ofis, sai wasu gungun yan daba dauke da muggan makamai suka tare musu hanya, a lokacin da Yansanda suka yi kokarin tunkarar yan daban ne sai Inspekta Haruna ya sauka don shawo kan yan daban dauke da bindigarsa.

“Kwatsam sai guda daga ciknsu ya dauki bulon Intalok ya buga ma Haruna a kai, nan take ya fadi sumamme, daga nan sai wasu suka dauki bindigarsa suka tsere, wanda hakan yasa Yansanda suka bude masa wuta, sai kuma wani harsashi da ya sami wani mutumi akan kuskure.” Inji shi.

Daga karshe Majia yace sun kama mutane shidda game da wannan rikici, kuma a yanzu haka suna cigaba da gudanar da bincike don gano bakin zaren. A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Kano ta kama mutane uku a unguwar Hotoro da laifin yin garkuwa da mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel