An dage shiga sansanin NYSC domin aikin bautar kasa saboda rigimar Kaduna
Mun ji cewa Hukumar NYSC wanda ke kula da dawainiyar hidimar kasa ta takadar da shirin horas da wani sahun masu bautar kasa a Jihar Kaduna kamar yadda da aka tsara a fara yau Litinin a fadin kasar.

Asali: Facebook
Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, an dage shiga sansanin horoswa na NYSC domin fara bautar kasa ne a dalilin rigimar da ya nemi ya barke a Kaduna. Yanzu dai Hukumar ta nemi ‘Yan Sahun ‘C’ su zauna a gida har sai an neme su.
A baya, Hukumar ta NYSC ta shirya cewa a Ranar 23 ga Wata ne za a fara horas da sababbin masu yi wa kasa hidima. Sai dai yanzu an tsaida wannan shiri a fadin Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya saboda halin tsaro da aka shiga.
KU KARANTA: An kwantar da masoyin Atiku da ya ketattaki tun daga Owerri a asibiti
A jiya ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sa takunkumi na hana yawo a cikin Birnin Kaduna da kewaye bayan rigimar da ta barke a cikin kasuwar magani wanda tayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 50 a Jihar.
Wannan ya sa NYSC ta fitar da jawabi cewa an dakatar da fara aikin horas da masu bautar kasa da aka turo Jihar kaduna. Har yanzu dai ba a sa ranar da za a kira wadanda za su yi wa kasar hidima ba inda aka nemi su cigaba da zaman gida.
Dazu kun ji cewa wani binciken da Jaridar Premium Times ta gudanar ya fallasa cewa Razak Atunwa wanda ke neman Gwamnan Jihar Kwara bai yi bautar kasa bayan ya kamalla karatu a kasar waje ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng