Mambobin APC sun yi zanga-zanga kan zaben fidda gwani a Katsina (hotuna)

Mambobin APC sun yi zanga-zanga kan zaben fidda gwani a Katsina (hotuna)

Daruruwan magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun fito unguwannin jihar Katsina don yin zanga-zanga kan tsarin zaben fidda gwani.

Legit.ng ta tattaro cewa magoya bayan jam’iyyar sun gudanar da zanga-zanga cikin lumana a mazabar Dustinma/Kurfi kan gudanar da zaben fidda gwani na majalisar dokokin kasar ba bisa ka’ida ba a jihar.

Da suka kai mamaya sakatariyar APC a karamar hukumar Dutsinma, masu zanga-zangan sun ce wasu dake ji da kari mulki sun yi yadda suka ga dama a zaben.

Mambobin APC sun yi zanga-zanga kan zaben fidda gwani a Katsina (hotuna)
Mambobin APC sun yi zanga-zanga kan zaben fidda gwani a Katsina
Asali: Facebook

Masu zanga-zangan wanda suka hada da maza da mata sun kasance dauke da kwalayen sanarwa darubutu daban-daban kamar: “Muna bukatar adalci daga APC shiyar Dutsinma Kurfi”. “Honarable Dallami Muhammad Kurfi muke so a matsayin dan takararmu a zaben 2019, ba adalci ba kuri’a”.

Mambobin APC sun yi zanga-zanga kan zaben fidda gwani a Katsina (hotuna)
Mambobin APC sun yi zanga-zanga kan zaben fidda gwani a Katsina
Asali: Facebook

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng