Yanzu-yanzu: Kotu ta hana belin Ayo Fayose, an dage karar zuwa Laraba

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana belin Ayo Fayose, an dage karar zuwa Laraba

- A safiyar yau ne aka gurfanar da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose gaban kotu a Legas bisa zarginsa da zambar kudi N30.9bn

- A yayin da ya gurfana gaban alkali, Fayose ya musanta aikata laifin da ake tuhmarsa da aikatawa

- Alkalin kotun ya bayar da umurnin a cigaba da tsare Fayose kuma ya daga karar zuwa ranar Laraba

Bayan kwashe kwanaki biyar yana amsa tambayoyi a hannun hukumar Yaki da Rashawa EFCC, an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a Babban Kotun Tarayya da ke Legas bisa zarginsa da zamban N30.8 biliyan.

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana belin Ayo Fayose, an dage karar zuwa Laraba
Yanzu-yanzu: Kotu ta hana belin Ayo Fayose, an dage karar zuwa Laraba
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da Fayose ne tare da kamfaninsa mai suna Spotless Investment Ltd inda ake tuhumarsa da aikata laifuka 11 masu alaqa ra zamba.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya ziyarci wuraren da rikicin Kasuwar Magani ya shafa (Hotuna)

Sai dai Fayose ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Bayan hakan, lauyansa, Kanu Agabi ya nemi kotu ta bayar da belinsa amma alkalin kotun CMA Olatoregun ya ki amincewa da bukatar bayar da belin inda ya bayar da umurnin EFCC ta cigaba da rike Fayose har zuwa ranar Laraba da za a cigaba da sauraron shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel