Bawa matasa kaso 40% na mukamai: APC ta farkewa Atiku laya, ta kafa ma sa hujja

Bawa matasa kaso 40% na mukamai: APC ta farkewa Atiku laya, ta kafa ma sa hujja

Dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya dauki alkawarin bawa matasa da mata kaso 40% na mukamai a gwamnatinsa idan har ya lashe zaben shekarar 2019.

Na yi alkawarin cewa, idan har Allah ya sa ku ka zabe ni, a kalla kaso 40% na mukaman da zan nada za su kasance matasa da mata,” in ji Atiku.

Atiku ya dauki wannan alkawarin ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Laraba, 17 ga waan Oktoba.

Sai dai a martani da APC, reshen kasar Ingila, ta fitar a shafinta na Tuwita, jam'iyyar ta bayyana cewar ikirarin na Atiku yaudara ce kawai don jan ra'ayin matasa tare da kalubalantar sa ya nuna matashi a cikin kwamitin sa na yakin zabe da ya kafa.

Bawa matasa kaso 40% na mukamai: APC ta farkewa Atiku laya, ta kafa ma sa hujja
Atiku
Asali: UGC

A ranar Talata ne kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya amince da nadin shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a matsayin wanda zai jagoranci kamfen din Atiku a fadin Najeriya.

Kazalika kwamitin ya amince da nadin Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, a matsayin wanda zai jagoranci kamfen din Atiku a shiyyar arewa maso yamma.

DUBA WANNAN: Atiku ya bayar da tallafin miliyan N10m ga wasu jama'a da iftila'i ya afkawa

Wannan sanarwar na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya fitar.

Sanarwar ta ce "PDP ta nada Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai, a matsayin shugaban yakin neman zaben Atiku na kasa.

"Mai girma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, zai jagoranci yakin neman zaben Atiku a yankin arewa maso yamma.

"Mai girma gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, zai jagoranci kamfen din Atiku a yankin arewa maso gabas.

"Samuel Ortom, gwamnan jihar Benuwe zai zama Sarkin yakin kamfen din Atiku a yankin arewa ta tsakiya," kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel