Takarar Atiku: PDP ta bawa Saraki, Tambuwal da Dankwambo manyan mukamai
Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya amince da nadin shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a matsayin wanda zai jagoranci kamfen din Atiku a fadin Najeriya.
Kazalika kwamitin ya amince da nadin Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, a matsayin wanda zai jagoranci kamfen din Atiku a shiyyar arewa maso yamma.
Wannan sanarwar na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya fitar.
DUBA WANNAN: Batan Janar Alkali: Mun gano fuskokin masu hannu cikin kisan sa - Hukumar Soji
Sanarwar ta ce "PDP ta nada Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai, a matsayin shugaban yakin neman zaben Atiku na kasa.
"Mai girma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, zai jagoranci yakin neman zaben Atiku a yankin arewa maso yamma.
"Mai girma gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, zai jagoranci kamfen din Atiku a yankin arewa maso gabas.
"Samuel Ortom, gwamnan jihar Benuwe zai zama Sarkin yakin kamfen din Atiku a yankin arewa ta tsakiya," kamar yadda sanarwar ta tabbatar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng