‘Dan takaran APC a Borno Zulum ya bayyana yadda yayi sana’ar kabu-kabu a baya

‘Dan takaran APC a Borno Zulum ya bayyana yadda yayi sana’ar kabu-kabu a baya

Farfesa Babagana Umar Zulum wanda shi ne ‘Dan takaran Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC a Borno ya bayyana yadda rayuwar sa ta kasance a da, da yadda ya kamo hanyar zama Gwamna a yanzu.

‘Dan takaran APC a Borno Zulum ya bayyana yadda yayi sana’ar kabu-kabu a baya
Babagana Zulum wanda ke takaran Gwamna a Borno ya taba aikin Direba
Asali: Getty Images

Babagana Umar Zulum ya bayyanawa Daily Trust a wata doguwar hira da su kayi cewa ya tashi ne a Kauyen Loskuri da ke Garin Mafa a Jihar Borno inda yace duk rana sai yayi tafiyar kilomita 7 wajen zuwa gona da kuma Makaranta.

‘Dan takaran Gwamnan yayi karatu ne a Garin Monguno daga 1975 zuwa 1985. Zulum yace a 1984 har zuwa kusan 1999 bai da sana’ar da ta wuce tukin mota inda ya shafe shekaru kusan 16 yana Direban kabu-kabu zuwa Garuruwa.

KU KARANTA: Allah ne ya zabi Atiku domin ceto Najeriya daga Buhari - Osuntokun

Wannan Bawan Allah yace a wancan lokaci ya kan tuka har manyan motocin itace daga daji domin samun na abinci. Farfesa Zulum yace har sai da ta kai ya koyi gyaran wadannan motoci da yake tukawa saboda tsabar sabo da aiki.

Babagana Zulum dai yayi karatun Difloma a Ramat Polytechnic da ke Maiduguri. Daga nan ne ya wuce Jami’ar Maiduguri ta Tarayya yayi Digiri. Daga nan ne kuma ya zarce yayi Digirgir a Ibadan kafin ya dawo ya zama Dakta a gida.

Ana kyautata zato Babagana Umar Zulum wanda babban Masani ne a bangaren fasahar noman rani kuma tsohon Kwamishinan Jihar Borno shi ne zai gaji Gwamna Kashim Shettima a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel