Fitaccen tsohon dan wasan Najeriya ya sadaukar da gidansa don kamfen din Buhari

Fitaccen tsohon dan wasan Najeriya ya sadaukar da gidansa don kamfen din Buhari

Tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya, Daniel Owefin Amokachi, ya sadaukar da wani babban gidansa dake kan titin Raba a garin Kaduna domin yakin neman zaben shugaba Buhari a zaben shekarar 2019.

Bayan sadaukar da gidan nasa, Amokachi, ya dauki alkawarin bayar da gudunmawa iya karfinsa wajen yiwa Buhari kamfen domin ya cigaba da zama shugaban kasar Najeriya har zuwa shekarar 2023.

An haifi Amokachi ne a watan Disamba na shekarar 1972 a garin Kaduna.

Amokachi na da tagwayen yara; Nazim Amokachi da Kalim, wadanda ya ce burinsa shine ya ga sun bugawa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wasa.

Fitaccen tsohon dan wasan Najeriya ya sadaukar da gidansa don kamfen din Buhari
Daniel Amokachi
Asali: Facebook

Fitaccen tsohon dan wasan Najeriya ya sadaukar da gidansa don kamfen din Buhari
Gidan da Amokaci ya bayar don kamfen din Buhari
Asali: Facebook

Bayan ya yi ritaya daga buga kwallon kafa, Amokachi ya zama mataimakin mai horar da 'yan wasan kwallon kafa ta Najeriya a shekarar 2007 da kuma tsakanin shekarar 2008 zuwa 2014 kafin daga bisani ya zama mai horar wa na wucin gadi daga shekarar 2014 zuwa 2015.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi II ya nada sabon dan masanin Kano (Hotuna)

Amokachi ya kasance dan wasan kwallon kafa Najeriya daga shekarar 1990 zuwa 1999.

A bangaren kungiyoyin kasashen ketare, Amokachi ya buga wasa a kungiyoyin daban-daban da suka hada da Everton, Club Brugge, Besiktas da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng