Da dumisa: Kuma dai! Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin Kano, Ogun da Zamfara

Da dumisa: Kuma dai! Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin Kano, Ogun da Zamfara

Shugaba Muhammadu Buhari, a yau, Juma’a ya kuma ganawa da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), hudu a fadar shugaban kasa dake Aso Villa, birnin tarayya Abuja.

Hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan ne a shafin sada ra’ayi da zumuntarsa na Tuwita da ranan nan.

Game da cewarsa, gwamnonin da suke halarce a ganawar sune gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, da gwamna AbdulAziz Yari na jihar Zamfara.

Amma Bashir Ahmed ya bayyana makasudin wannan ganawar nay au da Buhari ba. Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun yi has ashen cewa sun kara zuwa ganin Buhari ne kan rikicin zaben fidda gwanin jam’iyyar da yaki ci yaki cinyewa har yanzu.

Akwai babban matsala a jam'iyyar APC musamman kan zaben fidda gwanin gwamnan jihar Zamfara yayinda hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta ce jam'iyyar bata da dan takara a zaben 2019 sakamakon rikicin cikin gida tsakanin gwamna Yari da Sanata Marafa.

Mun kawo muku rahoton cewa Sanata mai wakiltan mazabar Zamfara ta tsakiya, Kabiru Marafa, ya ce babu ittifkin da akayi a zaben fidda gwanin kujeran gwamnan jihar karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Hukumar INEC ta aikawa jam’iyyar APC wasika cewa ta haramta mata fitar da dan takara a zaben gwamnan jihar Zamfara 2019 saboda rashin gudanar da zaben fidda gwani a jihar cikin lokacin da hukumar ta kayyade.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel