An kama wani dan kasuwa da ke safarar bindigogi daga kasashen waje zuwa Najeriya

An kama wani dan kasuwa da ke safarar bindigogi daga kasashen waje zuwa Najeriya

A jiya, Alhamis ne aka gurfanar da wani dan kasuwa, Ifeuwa Moses Christ a gaban babban kotun tarayya da ke Legas bisa zarginsa da safarar bindigogi daga kasar Turkey zuwa Najeriya.

Kamar yadda jami'an Kwastam suka bayyanawa kotu, Ifeuwa ya boye bindigogin ne cikin kwantena wadda aka rubutuwa cewar kayan ban daki ne ke ciki.

An gano cewar Ifeuwa da ke zaune a gida mai lamba 1 Ifeuwa Street, Ogidi ta jihar Anambra ya hada baki da wasu Ayogu Great James da ke zaune a Ploti mai lamba 291 Dawaki Extension a Gwarimpa Abuja da wani Emeka Umeh Festus wanda akafi sani da Amankwa domin say bindigogin.

An kama wani dan kasuwa da ke safarar bindigogi daga kasashen waje zuwa Najeriya
An kama wani dan kasuwa da ke safarar bindigogi daga kasashen waje zuwa Najeriya
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 12 da Obasanjo ya fadi a jawabinsa yayin ganawarsa da Atiku

Mai gabatar da kara a kotu, Mr Julius Ajakaiye ya shaidawa kotu cewar wadanda ake zargin sun hada baki daga ranar 6 zuwa 20 ga watan Satumba 2017 inda suka shigo da bindigogi 1570 zuwa Najeriya ta tashan ruwan Apapa da ke Legas ba bisa ka'ida ba.

Ya ce an siyo bindigogin ne daga birnin Istanbul da ke Turkey amma sai aka canja sunan kwantenen zuwa Guandong ta kasar China saboda batar da kama.

Sai dai wadanda ake zargi da aikata laifin sun musanta cewar sun aikata laifin.

Alkalin kotun ya bayar da umurnin a cigaba da tsare su a kurkuku sannan ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164