Yadda lantarki ta hallaka wani matashi da ya je sata a transiforma

Yadda lantarki ta hallaka wani matashi da ya je sata a transiforma

- Wani barawon wayoyin wutar lantarki ya gamu da ajalinsa a cikin transforma a Abuja

- Ya shiga cikin transforma ne da asuba amma kwatsam sai aka dawo da wutar lantarki kuma ta kona shi

- Daga bisani jami'an 'yan sanda da na kwana-kwana ne suka banbaro gawarsa daga jikin Pole wire

Rahoton da muka samu daga Sahara Reporters ya bayyana cewar wani mai welder, Innocent Ajayi ya rasa ransa yayin da ya shiga transiforma domin satar wayar wuta misalin karfe 4 na asubahim ranar Laraba a Kalabari Road da ke Karu Abuja.

Yadda lantarki ta hallaka wani matashi da ya je sata a transiforma

Yadda lantarki ta hallaka wani matashi da ya je sata a transiforma
Source: Twitter

Wani mazaunin yankin, Ahmed Mohammed ya ce Ajayi ya shiga transiformar domin ya satar wayar wutan kwatsam sai Hukumar Samar da Lantarki na Abuja suka dawo da wuta kuma wutar tayi sanadiyar mutuwarsa.

DUBA WANNAN: 2019: Ribadu ya janyewa Dankwambo takara

An gano cewar a baya Ajayi ya yi zaman gidan kurkuku saboda aikata laifi mai kama da wannan.

Ya bayyana cewar daga bisani ma'aikatan hukumar lantarki ne da taimakon jami'an kwana-kwana suka ciro gawar Ajayi da ya kone kurmus daga jikin Pole wire da ke kusa da na'urar dai-daita lantarkin wato transforma.

Kakakin Rundunar 'Yan sanda na yankin, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce mutumin ya mutu ne lokacin da ya ke kokarin satar wayoyin lantarki daga jikin transforma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel