Atiku ya fadawa fadar Shugaban kasa, BCO, da APC su maida hankali kan abin da ya dace ba zage-zage ba

Atiku ya fadawa fadar Shugaban kasa, BCO, da APC su maida hankali kan abin da ya dace ba zage-zage ba

Mun ji cewa Atiku Abubakar yayi wani kira na musamman ga Fadar Shugaban kasa, da kuma Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da Kungiyar BCO mai taya Shugaba Buari yakin sake neman zabe a 2019.

Atiku ya fadawa fadar Shugaban kasa, BCO, APC sa maida hankali kan abin da ya dace ba zage-zage ba

Atiku ya nemi Shugaban kasa Buhari ya fadawa Duniya aikin da yayi
Source: Facebook

‘Dan takarar Shugaban kasar a karkashin babban Jam’iyyar adawa ta PDP ya nemi Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC su daina sukar sa babu gaira babu dalilu su maida hankali game da abubuwan da ke gaban jama’a a 2019.

Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da jawabi ta ofishin sa a jiyan nan inda ya bayyana cewa tun da ya samu tikitin PDP ne fadar Shugaban kasar da wasun su, su ka taso sa a gaba domin kuwa Gwamnatin nan ba ta da abin fada ko kadan.

KU KARANTA: Kotu za ta janye belin da ta ba wani tsohon gwamnan PDP

‘Dan takaran na PDP yace har zuwa karshen 2014, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan-sa ya rika yabon sa. A wancan lokaci dai Buhari ya jinjinawa Atiku wanda sai kuma ga shi yanzu labari ya canza don za su kara a 2019.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya nemi Shugaba Buhari ya fito ayi zube-ban-kwarya na ayyukan Gwamnatin sa a maimakon a tsaya ana neman ci masa zarafi da kalamai marasa dadi. A 2019 ne dai 'Yan takaran za su kara.

A jiya kun ji cewa wasu hotuna na motocin kamfe dauke da hotunan 'Dan takarar na shugaban kasa watau Atiku ABubakar sun fara yawo a Gari kwanaki kadan bayan ya lashe zaben fitar da gwani a PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel