Na bar fiye da Naira Miliyan 300 domin a karasa kasuwa Oja-Oba – Fayose

Na bar fiye da Naira Miliyan 300 domin a karasa kasuwa Oja-Oba – Fayose

- Gwamna Jihar Ekiti Ayo Fayose ya fara shirin barin ragamar mulki

- Gwamnan yace ya bar wa Fayemi wasu kudi kuma bai bar bashi ba

- Jam’iyyar PDP ta su Fayose ta sha kasa ne a hannun APC kwanaki

Na bar fiye da Naira Miliyan 300 domin a karasa kasuwa Oja-Oba – Fayose

Gwamna Fayose yace ba ya fada da Kayode Fayemi
Source: Depositphotos

Mai Girma Gwamna Ayodele Fayose wanda yake shirin barin karagar mulki ya bayyana cewa ya bar kudi har Naira Miliyan 327 domin Gwamnatin da ke zuwa ta kasa ginin makekiyar kasuwar nan ta Oja Oba domin Ekiti ta amfana.

Gwamnan da wa’adin sa yake daf da karewa ya bayyana cewa ba zai shiga cikin rikicin Majalisar Jihar ba inda ‘Yan Majalisan APC su ka tsige Kakakin Majalisar dokoki Kola Oluwawole da Mataimakin sa Sina Animasaun a jiya.

KU KARANTA: Abin da ya sa ba zan je bikin rantsar da Fayemi ba - Fayose

Mai Girma Ayodele Fayose ya nemi ‘Yan Majalisan su ba Gwamna mai-shirin hawa mulki Kayode Fayemi duk goyon-bayan da ake bukata. Fayose yace bai so ya ji an fara kishin-kishin din tsige Fayemi idan ya dare kan kujerar mulki.

Ayo Fayose dai yace tun asali babu rigima tsakanin sa Fayemi, ya kuma bayyana cewa jama’a cewa bai bar wa Jihar Ekiti wani bashi ba inda yace tun da ya dawo Gwamna a 2014, bai ci bashi ba, sai dai tarin ayyuka da yayi wa Jihar ko ta ina.

Ba da dadewa bane dai kun ji Gwamnan mai shirin barin gado yayi barazanar ficewa daga Jam’iyyar sa ta PDP. Sai dai Ayodele Fayose ya nuna cewa babu abin da zai hada shi da Jam’iyyar APC mai mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel