Wani Mutum ya tsaya gaban Alkali tare da Surukarsa kan Gadon Matarsa
Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, wani Mutum Isah Sulaiman, ya gurfana gaban wata Kotun Shari'a ta Magajin Gari dake jihar Kaduna tare da surukarsa kan dambarwar gadon Matarsa da ta riga mu gidan gaskiya.
Sulaiman ya shaidawa kotun cewa, surukarsa, Khadija Ibrahim, ta yi mursisi wajen nannade gado na dukiya da kadarori da Matarsa ta bari nan duniya domin 'ya'yanta kwara uku.
Rahotanni sun bayyana cewa, Sulaiman wanda ke korafin surukarsa yana neman kotu akan ta kwato hakkin 'ya'yan su uku da Matarsa, Aisha, ra rasu ta bari.

Asali: UGC
Sai dai Surukarsa ta hau kujerar naki na ci gaba da danne wannan dukiya da cewar ai tuni wata kotun ta raba wannan gardama dake tsakanin su tun yayin rasuwar 'yar ta shekaru 3 da suka gabata.
KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Gwamnatin Tarayya za ta yaki duk wani mai kawowa zaman lafiyar Najeriya cikas
Ta ke cewa, surukin na tun bayan rasuwar 'yar ta da makonni uku ya garzaya gaban alkali inda aka rabon gadon kuma kowa ya kwashi rabonsa bisa tsari da kuma tafarki na addinin Islama.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, alkalin kotun, Musa Sa'ad, ya nemi su gabatar da takardu na shaidar rabon gadon da waccan kotun ta gudanar inda kuma ya daga sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Okotoba.
Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng