2019: Ribadu ya janyewa Dankwambo takara

2019: Ribadu ya janyewa Dankwambo takara

- Gwamna Ibrahim Hassan Danlwambo ya karbe tikitin takarar Sanata na Gombe ta Arewa bayan ya sha kaye a takarar shugabancin kasa na PDP

- Hakan ya faru ne bayan wanda ya lashe tikitin, Mohammed Usman Ribadu ya janyewa Dankwambo takarar

- Ribadu ya ce Dankwambo ne yafi cancanta ya wakilci Gome ta Arewa saboda irin rawar da ya taka a shekaru 7 na mulkinsa

Dan takarar Sanata karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na mazabar Gombe ta Arewa, Mohammed Usman Ribadu ya janye takararsa kuma ya mika tikitin takarar ga gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo.

2019: Ribadu ya janyewa Dankwambo takara
2019: Ribadu ya janyewa Dankwambo takara
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari

A jawabin da ya yi wajen taron maraba ga gwamna Dankwambo bayan dawowarsa daga babban taron jam'iyyar PDP da akayi a Port Harcoiurt, Ribadu ya ce ya janye takararsa ne saboda Dankwambo ne wanda ya fi cancanta ya wakilci Gombe ta Arewa a majalisar tarayya.

A cewarsa, Dankwambo ya cancanci ya yi takarar kujerar Sanatan saboda irin ayyukan cigaba da ya samar a jihar Gombe cikin shekaru bakwai da suka gabata na mulkinsa.

A baya, majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar tun farko dama Dankwambo ya zabi Ribadu ya yi masa takara ne a matsayin shirin ko ta kwana idan bai yi nasarar samun tikitin takarar shugabancin kasa na PDP ba.

Gwamna Dankwambo ya samu kuri'u 111 inda ya zo na biyar a zaben fidda gwani na jam'iyyar ta PDP da aka gudanar a Port Harcourt babban birnin jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164