Masana sun bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai zabura a nan gaba

Masana sun bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai zabura a nan gaba

- Ana tunani abubuwa za su kara kyau a Gwamnatin Shugaba Buhari

- Masana tattalin arziki sun ce Najeriya ta dai kama hanyar tudun-tsira

Masana sun bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai zabura a nan gaba
Tattalin arzikin Najeriya yana kara mikewa a Gwamnatin Buhari
Asali: UGC

Mun samu labari cewa ana sa ran za a ga cigaba a bangaren tattalin arzikin kasa a Gwamnatin nan ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yanzu ma Masana su kace ana ganin motsi a Kasar duk da irin manyan cikas da ake samu.

Daily Trust ta rahoto masana harkar tattali irin su Raji Rasaki su na nuna cewa abubuwa sun kama hanyar mikewa a kasar. Masanin yace akwai bukatar Najeriya ta cigaba da kokarin wajen fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen ketare.

Rasaki yace asusun kasar wajen Najeriya yayi kasa ne bayan da matsalar rashin aikin yi ya soma raguwa a Kasar Amurka kamar yadda alkaluma su ka nuna. Hakan ya jawo Dalolin Amurkar da Najeriya ta mallaka ya sauka kasa kwanan nan.

KU KARANTA:

Lanre Popoola wanda shi ne Shugaban Kungiyar MAN yace babu dalilin tada hankali a Najeriya don kudin kasar wajen ta yana raguwa domin kuwa farashin gangar mai yana kara kudi sannan kuma ana samun shigowar kudin da aka sace a da.

Tunji Adepeju wanda shi ma Masani ne ya nuna cewa Najeriya tana kan hanya a fuskar tattali inda yace nan gaba abubuwa za su kara kyau. Adepeju ya yabawa yarjejeniyar da aka shiga tsakanin Najeriya da Kasar Sin inda yace za a amfana kwarai.

A cikin kwanakin nan dai an samu aikin yi a bangarorin kiwon lafiya da bangaren sufuri da sauran su a Amurka wanda hakan yake da tasari a Najeriya. Sai IMF dai tana ganin kasar har yanzu da sauran ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng