Na yi matukar mamakin yadda Atiku ya zama dan takarar PDP - Obasanjo

Na yi matukar mamakin yadda Atiku ya zama dan takarar PDP - Obasanjo

Akasin yadda wasu kafafe yadda labarai suka wallafa cewar tsaffin shugabanin kasar Najeriya tare da gwamnonin PDP da wasu Janar-Janar din Soja ne suka mara wa Atiku baya ya yi nasarar zama dan takarar PDP, Obasanjo ya ce ya yi mamakin nasarar Atiku kuma baya goyon bayansa.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi mamakin yadda tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kamar yadda wata majiya ta sanar da Daily Trust.

Na yi matukar mamakin yadda Atiku ya zama dan takarar PDP - Obasanjo
Na yi matukar mamakin yadda Atiku ya zama dan takarar PDP - Obasanjo
Asali: UGC

Atiku yana daya daga cikin 'yan takara 12 da suka fafata a zaben fidda gwanin na PDP da aka gudanar a Pot Harcourt ta Jihar Rivers inda galibin masu nazarin al'amuran siyisa suka yi hasashen Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ne zai lashe zaben.

DUBA WANNAN: 2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

Sai dai bayan an sanar da cewar Atiku ne ya yi nasara, kafafen yada labarai da dama sun ruwaito cewar tsaffin shugabanin kasa na Najeriya da wasu Janar-Janar din Soja ne suka yi wata ganawar sirri suka yanke shawarar goyon bayan Atiku.

An ce tsohon shugaban mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida, Abdulsalami Abubakar, Janar TY Danjuma, Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo da sauran gwamnonin PDP ne suka amince da mara wa Atiku baya.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ce Obasanjo ya yi mamakin nasarar da Atiku ya yi kuma ya ce baya goyon bayan Atiku kana baiyi wani taro da tsaffin shugabanin Najeriya domin goyon bayan Atiku ba. Hasali ma, Obasanjo ya sha fadin cewar idan ya goyi bayan Atiku, Allah ba zai yafe masa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel