Lauretta Onochie ta yi kaca-kaca da Jagoran Mabiya Katolikan Najeriya Olasupo

Lauretta Onochie ta yi kaca-kaca da Jagoran Mabiya Katolikan Najeriya Olasupo

Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan kafafen sadarwa na zamani watau Misis Lauretta Onochie ta dauki dogon lokaci tayi kaca-kaca da Shugaban Kungiyar kiristoci na CAN.

Onochie ta caccaki Shugaban Kungiyar CAN

Misis Onochie ta yi kaca-kaca da Samson Olasupo wanda shi ne Jagoran Mabiya Darikar Katolika ta Kiristocin Najeriya. Onochie ta nemi Shugaban Kungiyar ta CAN da yayi koyi da irin su Rabaren Ejike Mbaka da Fasto WF Kumuyi.

Hadimar Shugaban kasar ta nemi Dr. S. Olasupo ya dauki darasi wajen sauran Limaman gaskiya na Allah inda tayi kira ga Babban Malamin na Kiristocin kasar da ya daina karya yana jawo abubuwan da ka iya jefa kasar nan cikin matsala.

KU KARANTA: Shugabanin dariqar Qadiriyyah sun ziyarci Buhari a Villa

Onochie ta aikawa Shugaban CAN din sako ne ta wata budaddiyar wasika a shafin ta na Facebook. Mai ba Shugaban kasar shawara ta ma zargi Shugaban Kungiyar ta CAN da karbar kudin sata daga manyan Kasar nan da sunan gudumuwa a lokacin PDP.

Kwanakin baya ma dai Lauretta Onochie ta dura kan Kungiyar ta Kiristocin Najeriya CAN tace su ke hura wutan rikicin Yankin Benuwe da Filato da sauran wuraren da ake rigima a Arewacin kasar nan

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel