A kai kasuwa, bama bukata - Sakon APC ga gwamnan dake shirin fita daga PDP

A kai kasuwa, bama bukata - Sakon APC ga gwamnan dake shirin fita daga PDP

Jam'iyyar APC reshen jihar Ekiti ta shawarci gwamnan jihar mai barin gado, Ayodele Fayose, da tun wuri ya nemi jam'iyyar da zai koma idan ya fita daga PDP.

Shugaban jam'iyyar APC a jihar Ekiti, Cif Paul Omotoso, ne ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya fitar yau, Talata, a garin Ado Ekiti.

"Kada ma Fayose ya fara tunanin shigowa jam'iyyar APC ba tare da ya gurfana gaban kotu domin amsa laifukan dake wuyansa ba," a cewar Omotoso.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Omotoso na wadannan kalamai ne a matsayin martani ga barazanar da Fayose ya yi na ficewa daga jam'iyyar PDP.

A kai kasuwa, bama bukata - Sakon APC ga gwamnan dake shirin fita daga PDP
Ayo Fayose
Asali: Depositphotos

Fayose ya yi barazanar fita daga PDP ne bayan an sanar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar da ya lashe zaben cikin gida na jam'iyyar da aka yi a garin Fatakwal a karshen mako.

Dan takarar da Fayose ke goyon baya, Aminu Waziri Tambuwal, ya zo na biyu da adadin kuri'u 693 a zaben.

A jawabinsa, Omotoso, ya bukaci Fayose ya fara wanke kansa a kotu kafin ya fara tunanin canja sheka zuwa APC.

"Ba zamu taba karbar Fayose ba, bata jam'iyya yake yi ba gina ta ba. Ya tafi wani wurin, amma ba APC ba.

DUBA WANNAN: Tsohon IG da APC ta hana takara ya jagoranci addu'ar Allah-tsine a hedkwatar jam'iyya

"Ko a ranar 4 ga watan Nuwamba na shekarar nan sai ya gurfana a gaban kotu bisa tuhumar sa da almundahana.

"Ba zai yiwu mu karbe shi a APC ba, jam'iyyar mu ba mafaka ba ce ga masu laifi da karya ba.

"Jam'iyyar APC ta mutane ce masu kima da mutunci, mutane irinsu Fayose basu dace da manufofi da akidar APC ba," a cewar Omotoso.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewar duk kokarinsa na jin ta bakin Fayose bai tasiri ba saboda layukan wayarsa a kashe su ke, kazalika hadimansa sun ki cewa komai a kan kalaman na jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng