Yadda wasu yan fashi da makami suka yi ma jami’in Dansanda kisan gilla a Kalaba

Yadda wasu yan fashi da makami suka yi ma jami’in Dansanda kisan gilla a Kalaba

A yanzu haka rundunar yansandan jahar Krosribas na cikin zaman jimami yayin da kwamishinan yansandan jahar, Hafiz Inuwa Muhammed ya tabbatar da cewa wasu yan fashi da makami sun bindige wani jami’in dansanda, Ebri Ogban.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, Irene Igbo ce ta sanar da mutuwar dansanda Ebri a madadin kwamishinan yansandan jahar, inda tace lamarin ya faru ne a garin Kalaba.

KU KARANTA: Jami’ar Karaduwa: Shahararren dan siyasa zai gina jami’a da kwalejin kimiyya a jahar Katsina

“Mun samu rahoton wasu yan fashi da makami na yi ma wasu jama’a fashi a unguwar Otop Abasi dake cikin garin Kalaba, nan da nan jami’anmu suka dira unguwar da nufin kama yan fashin, sai dai tsautsayi ta rutsa da Ebri inda suka bindigeshi yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida ba tare da sanin abinda ke faruwa ba.” Inji ta.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa dansandan na hanyarsa ta zuwa gida ne bayan ya tashi daga wajen aikinsa a lokacin da yan fashin suka bindigeshi.

“Ba shi da masaniya game da abin dake faruwa, yana kan hanyarsa ta zuwa gida ne kawai sai yan fashin suka halaka shi.” Inji Goodnews Etim.

A wani labarin kuma wasu gungun yan fashi da makami sun yi garkuwa da mata guda biyu tare da kashe wani mutumi a layin mahuta dake garin Tabanni cikin karamar hukumar Birnin Gwari ta jahar Kaduna.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto rundunar Yansandan jahar Kaduna bat ace uffan ba game da lamarin daya faru.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel