Gwamnatin tarayya zata sanar da sabon karin albashi – Shugaban kungiyar kwadago

Gwamnatin tarayya zata sanar da sabon karin albashi – Shugaban kungiyar kwadago

- A satin da ya gabata ne kungiyar kwadago ta kasa ta janye daga yajin aikin jan kunne da ta shiga a kan batun Karin albashin ma’aikata

- Kungiyar ta kwadago ta janye yajin aikin da ta shiga ne domin bawa kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa a kan Karin albashi ya kamala aikinsa

- Shugaban kungiyar kwadago, Ayuba Wabba, ya shaidawa manema labarai yau, Litinin, a Abuja cewar gwamnatin tarayya zata sanar da sabon Karin albashi

A yayin da kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa ya kammala aikinsa, gwamnati ta kammala shirin sanar da sabon karin albashi da zata yiwa ma’aikata.

Tuni kwamitin ya mika rahoton aikinsa ga shugaban kasa Muhammadu, kamar yadda shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba, ya sanar da manema labarai yau, Litinin, a Abuja.

A cewar Wabba, kwamitin ya yi zama na kwanaki biyu domin kara tattaunawa a kan sabon karin albashin da za a yiwa ma’aikata, wanda ma’aikata da kungiyar kwadago zasu amince da shi.

Gwamnatin tarayya zata sanar da sabon karin albashi – Shugaban kungiyar kwadago
Shugaban kungiyar kwadago, Ayuba Wabba
Asali: Depositphotos

Ina mai tabbatar wa da ma’aikatan Najeriya cewar an kamala dukkan shiri da bin dukkan hanyoyi domin Karin albashi, yanzu haka an mika rahoto kuma za a saka masa hannu cikin wannan satin.

DUBA WANNAN: Martanin Obasanjo a kan nasarar Atiku a zaben fitar da dan takarar PDP

Ina son yin amfani da wannan dammar domin yin kira ga masana’antu, kamfanoni da dukkan wuraren aiki da ban a gwamnati ba, da su daure su biya ma’aikatan su mafi karancin albashin da gwamnati zata yanke,” a cewar Wabba.

A satin da ya gabata ne kungiyar kwadago ta janye yajin aikin jan kunne da ta shiga a kan batun yin Karin albashi ga ma’aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel